Buhari ya kyauta da ya sadaukarwa da M.K Abiola ranar dimokradiyya da lambar GCFR, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Ai wannan lambar girmamawa ta GCFR tuntuni gwamnatocin baya yakamata su bawa Marigayi Mashood Kashimawo Olawale Abiola ballantana kuma kayi maganar mayar da ranar June 12 a matsayin ranar tunawa dashi a Najeriya.

Duk wanda ya kai shekara 35 a kasarmu yasan cewa Jamhuriya ta uku lokacin mulkin Babangida abubuwa sun faru kamar almara saboda jamhuriyar ba cikakkiya bace don siyasar a iya kwankwason Najeriya take amma daga wuyanta zuwa kai ba dimokaradiya bace.

Kowa ya gani ko kuma ya karanta, zaben da akayi a June 12, tsakanin Alhaji Bashir Usman Tofa da kuma Alhaji M.K Abiola,wanda saboda son zuciya a shekarun baya wasu suke ce masa shine yafi ko wani zabe kyau a Najeriya; Abiola ne yaci amma saboda gwamnatin mai ci ta soja bata da ra’ayinsa sai karshe aka canja sakamako bayan kuma ya nuna bai yadda ba aka kamashi.

A wannan maganar babu bukatar kawo reference saboda abu ne wanda ya faru a idon duk dan Najeriyan da ya kai shekarun dana fada a baya.Kuma a wancen lokacin anji tsoro kada a samu rikicin siyasa tsakanin kabilar Yarabawa da kuma Hausawa. Abunda ya faru ya kawo cacar baki a jaridu da gidajen radiyo da talabijin tsakanin Kudu da Arewacin Najeriya saboda su Yarabawa suna gani kamar damarsu ce ta farko su mulki Najeriya duk da wasu da yawa daga Kudu din basa yinsa saboda suna kallonsa kamar yafi karkata ga Arewa. Amma kwace zabensa da akayi yasa Yarabawa sun dunkule waje daya wajen nuna bacin ransu.

Akwai jita-jitan cewa, bayan da gwamnatin Abacha tazo, a kokarin samar da zaman lafiya ta nemi Abiola ya bada sunayen mutanen da yakeso ayiwa ministoci. Wanda wasu suna ganin har zuwan Obasanjo ma a 1999 kamar rarrashi ne gasu saboda Najeriya tayi musu ba daidai ba. Don bazan taba mantawa ba, bayyana cewa Abiola ya fadi ya kashe jikin da yawa daga cikin ‘yan Arewa wadanda ma ba ‘yan siyasa bane.

Tabbas mutane irinsu Mashood Kashimawo Olawale Abiola sun cancanci a ware musu rana guda don tunawa dasu duba da irin gwagwarmaya da yayi wajen samawa kasar Najeriya suna a idon duniya.

Abiola ya fara siyasa tun yana shekara sha tara, yana cikin matasa da suka fara shiga jam’iyar National Council of Nigeria and the Cameroon (NCNC) tun kafin kasar Kamaru ta fita. Jam’iyar NCNC itace ta farko wajen gwagwarmayar neman ‘yancin kai, sannan tana cikin jam’iyun da suka hada kai wajen samar da shugaban kasa na farko a Najeriya.

Abiola ya tashi cikin jajircewa a rayuwarsa don ganin ya dauki rayuwar gidansu da kuma rayuwarsa a matsayinsa na matashi. Hakan ne yasa har ice (firewood) ya siyar kafin daga baya ya koma aikin raba abinci wajen taro ko biki ko kuma dakin siyar da abinci. Da wannan sana’a ce ya dauki nauyin karantunsa na sakandare. Daga baya Allah yayi masa arziki,dukiyarsa ta yiwa mutanen Najeriya da Afrika rana saboda ya rayu ne wajen gina al’umma da samar da ayyukan yi a nahiyar Afrika.Ya mutu 1998, yana da shekara 60 a duniya. Ya bar masana’antu masu zaman kansu wadanda dimbin mutane suke aiki a cikinsu. Ina bada shawara, bayan ware ranar tunawa dashi gwamnati ta biya zuri’arsa kudin da yayi asara wajen takara a June 12.

Allah ya hadamu dashi a aljanna.

Share.

game da Author