Mataimakin gwamna, Wakkala, ya raba kayan abinci ga mabukata a Zamfara

0

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Ibrahim Wakkala ya raba wa mabukata 11,000 abinci a jihar.

Wakkala ya raba kayan abinci,tufafi da kudade wa marayu, matan da basu da aure da wadanda suka rasa mazajen su, matasa, sannan da nakasassu a gidan sa dake Gusau.

Ya ce ya yi haka ne domin tallafawa wa tallakawa musamman yadda hakan na daya daga cikin koyarwar musulunci.

” Zan raba tufafi, kayan abinci da kudi wa marayu da talakawa 1000 domin su sami yin shagalin Sallah.”

A karshe ya yi kira ga attajirai da ‘yan siyasan kasar nan da su taimakawa talakawan kasar nan domin a sami saukin rayuwa.

Share.

game da Author