Tsohon babban jojin Najeriya, Alpha Belgore ya soki lamirin gwamnatin Buhari da ba marigayi Abiola lambar girmamawa wadda ta fi kowacce daraja a kasar nan
Belgore ya ce dokar kasa ba ta ba shugaban kasa damar yin haka ba domin wannan lambar girmamawa ba a ba wanda ya rasu sai dai idan karrama shi za ayi akan mai da wani ginin gwamnati a nada mata sunan sa.
Belgore da yake zantawa da PREMIUM TIMES ta wayar tarho, ya ce wannan lambar girmamawa ta GCFR, akan ba shugaban kasa ne kawai wanda yake raye sai kuma jarumin soja da ya rigamu gidan gaskiya shima akan yi masa wannan karramawa amma ba haka kawai a lika wa wani ba.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya canza ranar murna da hutun dimokradiyya a kasar nan zuwa ranar 12 ga watan Yuni daga 2019.
Buhari yayi haka ne domin ya karrama marigayi Abiola da ake zaton shine ya lashe zaben 12 ga watan Yuli din da shugaban kasa a wancan lokacin Ibrahim Babangida ya soke zaben.
Bayan haka shugaba Buhari ya ce zai bai wa marigayi Abiola babbar lambar girmamawa ta GCFR wanda babu wanda yake samun wannan lambar girmamawa sai tsohon shugaban Kasa wanda hakan ya nuna kamar Abiola ma tsohon shugaban kasa ne.
Mataimakin Abiola a takarar wato Ambasada Babagana Kingibe shima za a bashi lambar girmamawa na GCON.

Sannan kuma da fitaccen lauyan nan, marigayi, Gani Fawehenmi za a bashi lambar yabo na GCON.
Za ayi bukin mika wadannan lambobin yabo da girmamawane a ranar 12 ga watan Yuni mai zuwa.
A dalilin haka daga shekara mai zuwa za a yi hutun dimokradiyya ne daga ranar 12 ga watan Yuni.
Discussion about this post