Mafi yawan mata, mazajen su ke yin sanadiyyar rayukan su – Amina Mohammed

0

Mataimakiyar babban Sakataren majalisar dinkin duniya Amina Mohammed ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa daya cikin mace biyu da ake kashewa masoya ko abokanan su maza ne ke kashe su.

Ta fadi haka ne a taron hada kawance domin samun madafa kan matsalolin da ya shafi muzgunawa mata tsakanin majalisar dinkin duniya (UN) da kungiyar tarayyar turai (EU) da aka yi a kasar Brussels.

Amina ta ce bayanan binciken sun kara nuna cewa matan dake fama da irin wadannan matsalolin kan nemi taimako wurin likitoci ko kuma wurin jami’an tsaro amma sai dai kash, basu samun haka saboda tsoron saba wa addini ko kuma kauce wa al’adan da aka tashi akai.

Ta kara da cewa domin kubutar da mata daga cikin irin wadannan kangi kamata yayi duniya ta maida hankali wajen bude wa mata kofofin sauraren su da duk irin taimakon da za a iya sama musu saboda gujewa fadawa wadannan matsaloli.

” A yanzu haka kungiyar Tarayyar Turai ta yi hubbasa domin taimakawa mata sai dai abin da kamar wuya domin sai ankafa dokoki da za su samar musu da kariya, tsaro da yaye musu talauci sannan ne za a iya cimma nasara kan haka.

Share.

game da Author