Na kwarara wa mijina ruwan zafi ne saboda azabtar da ni da yake yi

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gurfanar da wata mata da aka samu da laifin kwarara wa mijinta ruwan zafi a jikin sa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imohimi Edgal ya bayyana cewa matar mai suna Joy Imeribe mai shekaru 32 ta aikata haka ne a daidai suna shirin yin karin kumallo.

Joy ta bayyana mana cewa a ranar Talata 29 ga watan Mayu mijinta Ike ya lakada mata duka bayan ta dawo daga kasuwar siyar da gwanjunan kaya da take yi.

Ta ce bayan dukan da ya lakada mata ya kulle ta a cikin daki inda sai da garin Allah ya waye sannan ya bude ta.Bayan gari ya waye duk da haka bai kyale ta yayi ta neman ta da fada, toh a nan ne fa ta fusata ta dauko ruwan zafi ta kwarara masa a jiki.

Edgal ya ce Joy da Ike basu yi aure ba amma suna da ‘ya’ya hudu maza hudu yanzu haka tana dauke da cikin wata daya.

Share.

game da Author