Yadda Adamu ya kashe Budurwar sa da wuka saboda an hana shi aurenta

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe Abdulmaliki Sumonu ya bayyana wa manema labarai a garin Damaturu cewa rundunar sa ta kama matashin nan mai suna Muhammed Adamu da ya kashe budurwar sa
da wuka.

Sumonu ya ce Adamu ya aikata haka ne ranar 29 ga watan Mayu, daga bisani kuma ya gabatar da Adamu gaban ‘yan jaridar domin ya bayyana yadda ya kashe Hauwa da kan sa.

Daga nan ne fa sai Adamu ya fara fetso zance kamar haka.

” Suna na Muhammed Isa Adamu dan karamar hukumar Potiskum. Mun fara soyayya da Hauwa tun a shekarar 2014, shekaru hudu kenan.

” A lokacin da muke tare da Hauwa na fara shan miyagun kwayoyi wanda har wata rana na nemi taimako a asibitin Azare dake jihar Bauchi domin in daina wannan mummunar dabi’a.

” Hauwa mace ce mai matukar biyayya domin bata taba saba mun ba.

” Mun fara samun matsala ne tun da ga lokacin da iyaye na suka ki amincewa in aure ta, sannan kuma na fahimci cewa ta sami wani sabon saurayi.

” Hauwa ta fada mini cewa tun da iyaye na sun ki amincewa mu yi aure kamata ya yi in kyale ta ta auri wani.

” Ta na fada min haka kuwa sai naji zuciya ta fara tafarfasa , na rasa in da zan sa kai na kawai sai na yanke hukuncin in kashe ta sannan in kashe kai na kowa ya huta.

” Kafin na hadu da Hauwa a wannan rana sai da na yi tatul da kwayar da na saba sha ‘Exol’ sannan muna tare da ita na zaro wuka na ko daba mata. Daga nan ne fa ni ma na yi kokarin daba wa kai na wukar amma a haka jini na malala daga jikin ta ta hani.

” Hauwa ta yi ta roko na kada in kashe kai na sannan in nemi gafarar Allah kan abin da nayi mata duk kafin a zare ran nata.

Bayanai sun nuna cewa Adamu ya kammala karatun sa a kwalejin koyar da malunta dake Potiskum.

Share.

game da Author