Auwal Kasimu mai shekaru 35 ya maka matar kawunsa Bilkisu Abdullahi a kotu saboda damun sa da take yi da karar injin din markade.
Kasimu ya bayyana wa kotu cewa karar injin din na hana su sakat a gidan na su sannan ya na hana mahaifiyar sa sukuni.
” Tun da mahaifiyata ta kamu da hawan jini likita ya hore mu da mu killa ce ta a wuri da babu irin wadannan kararraki.
Kasimu yace Bilkisu bata tsaya nan ba, har kaji take kiyo a gidan.
Ya ce ya shigar da kara ne bayan kawun nasa wato mijin bilkisu mai inji ya ki daukar mataki a kai.
Ita kuwa Bilkisu ta bayyana a kotu cewa babu yadda za ta iya rabuwa da wannan inji nika domin da shi suke ci suke kuma sha.
” Mijina ba shi da koshin lafiyar da zai iya fita ya je ya nemo sanna kuma Kaji da yai magana akai duk safe na kan kora su waje ne su je su kiwon sai da yamma su dawo.
Daga karshe dai alkali Musa Sa’ad ya hore su da su koma gida su zauna lafiya sannan ya yanke hukuncin cewa kotu za ta ziyarci gidan domin duba halin da gidan ke ciki.
An daga ci gaba da sauraren karan zuwa watan gobe.