‘Yan Najeriya na busa karar taba sigari biliyan 20 duk shekara

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa a shekara ana shan karar taba sigari har biliyan 20 a Najeriya.

Ya fadi haka ne ranar Litini a Abuja a taron wayar da kan mutane game da illolin shan taba sigari wanda ake yi duk shekara.

Adewole yace abin da ya fi ci masa tuwa a kwarya shine yadda sama da mutane miliyan 4.5 dake shan taba sigari ke yi musu illa a jika kuma duk da haka suna busa ta.

” A shekarar 2015 bincike ya nuna cewa Najeriya ta yi asaran dala biliyan 7.6 wurin kula da mutanen da suka kamu da cututtukan da ake kamuwa da su sanadiyyar busar taba sigari. Bayan haka kuma yanzu har wata samfarin bushe bushe ne aka kirkiro kuma wai shisha duk domin cutar da mutane.

Adewole yace lokaci ya yi da gwamnatin kasar nan za ta karfafa hana amfani da taba sigari ta kowace iri domin ceto rayukan mutanen ta.

Sannan kuma an gano cewa shan taba na rage yawan tsawon shekarun da mutum zai yi da shekaru 15.

Share.

game da Author