Wasu likitoci dake jami’ar ‘St. Louis’ sun bayyana cewa masu fama da tabuwar hankali sun fi masu cikakken hankali yawan shan taban sigari.
Likitocin sun gano haka ne a bincike da suka yi kan wasu dake fama da tabuwar hankali da ake kula da su. A nan ne suka ga cewa lallai masu dan matsala a kwakwalwar su sun fi shan taba fiye da wadanda ba haka ba.
Jagoran binciken Li-Shiun Chen ya ce mafi yawan masu shan taba suna son su bari amma hakan ya gagara. Sannan kuma idan har ma sun warke daga cutar ma rabuwa da tabar ya kan gagara.
Li-Shiun Chen ya yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya na asibitocin mahaukata da su taimaka musu wajen ganin sun kubuta daga wannan dabia wato shan taba sigari.
Discussion about this post