Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Operation Lafiya dole’ Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya da hadin gwiwar jami’an tsaron kasar Kamaru sun yi nasarar kashe ‘yan Boko Haram 10 a wani arangama da suka yi a kauyen Ngelkona dake karamar hukumar Ngala jihar Barno.
Onyema ya sanar da haka ne ranar Lahadi a Maduguri inda ya kara da cewa jam’ian tsaron sun yi arangama da Boko Haram din ne da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar.
‘‘Mun fatattaki Boko Haram din da suke kan dawakai sannan mun kwace makaman su da suka hada da bindigogi, kwari da baka, Wayar salula biyu da fasfo din tafiya na kasar Kamaru a hannun su.
Bayan haka Nwachukwu ya bayyana cewa dakarun sojin sun sake yin arangama da wasu Boko Haram din a kauyen Ngoshe dake karamar hukumar Gwoza.
Ya ce sun kwace bindiga daya,harsasai da bama bamai hudu.
A karshe Nwachukwu ya ce bayan haka dakarun sojin sun sake yin batakashi da wasu ‘yan Boko Haram a dajin Yaridiri dake karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.
Onyema ya ce sun kwace harsasai bindiga da dama, babur guda daya, wayar salula biyu sannan da tsabar kudi da ya kai naira 2,280,000 a hannun su.
Discussion about this post