1 – Jami’an ‘yan sanda su mai da hankali wajen samar da zaman lafiya a kasar nan da kuma tabbatar da tsaro ga kowani dan Najeriya
2 – Dole a dakatar da tsangwamar da ake yi wa ‘yan adawa da wadanda ba su ra’ayi daya da gwamnati mai mulkida ya hada da wasu daga cikin ‘yan majalisa da alkalai da sauran su.
3 – Dole ne abi dokar kasa sauda kafa sannan da kuma hana jami’an gwamnati ci gaba da muzguna wa ‘yan Najeriya babu gaira babu dalili.
4 – Dole shugaban kasa ya hukunta duk wani jami’in gwamnati da ke neman ya yi amfani da ofishin sa wajen cin mutuncin wasu da tozarta wannan dimokradiyya da muke rayawa a kasar nan.
5 – Dole gwamnati ta dawo daga rakiyar nuna fifiko a yaki da cin hanci da rashawa da ta ke yi, da wasu suka zama shafaffu da mai, wasu ko ‘ya’yan kaji. A binciki har da wadanda ke cikin gwamnati suma ba ana yi wa wasu bita da kulli ba.
6 – Dole ne a samar wa majalisar Kasa kariyar da take bukata da yin nesa da shiga al’amurorin majalisar. Sannan a attabata an kamo wadanda suka sace sandar iko na majalisa.
7 – Majalisar kasa za ta hada hannu da hukumomin gwamnatocin kasashen duniya da kungiyoyi masu zaman kansu domin ingata ayyukan majalisa da sake yin dashe mai inganci ga turbar dimokradiyyar kasar nan dake tangal-tangal.
8 – Shugaban kasa yayi maza-maza wajen samar wa ‘yan Najeriya mafita ga wannan bakin talauci da ake fama dashi da rashin aikin yi ga matasan kasar nan musamman yanzu da gangar danyen mai ya zarce $80
9 – Bayan haka majalisa za ta hada hannu da kungiyoyin kare hakkin jama’a da masu zaman kan su domin cetowa da inganta dimokradiyya a Najeriya.
10 – A yau dukkan mu ‘yan majalisa mun jaddada goyon bayan mu da yin mubaya’a ga shugabannin majalisar.
11 – Sannan kuma muna nan a kan bakar mu da nuna fushin mu da rashin jin dadin mu ga sufeto janar din ‘yan sandan Najeriya, na kin samar wa ‘yan Najeriya tsaron da ya kamata. Da kuma kala wa wadanda ba ya so a kasa sharri babu gaira babu dalili.
12 – Idan har ba a bi umarnin mu ba za mu yi amfani da karfin ikon da doka ta bamu domin yin abin da ya dace.