An dawo wa Saraki da wasu daga cikin masu tsaron sa

0

Rahotannin da ya iske mu da safiyar Talata din nan sun nuna cewa an dawo wa shugaban majalisar Dattawa Bukola Sarki da wasu daga cikin masu tsaron sa da aka janye daga ci gaba da tsare Saraki din.

Gwamnati ta janye kusan duka masu tsaron shugaban majalisar da wadanda suke tare da kakakin majalisar wakilai, da mataimakan su duka.

Ko da yake a bayanan da PREMIUM TIMES ta samu a yau sun nuna jami’an tsaro biyar ne kacal aka maida wa Saraki sannan har yanzu bamu tabbatar ko shi ma kakakin majalisar wakilai da mataimakin sa Lasun an mai da musu da nasu masu tsaron.

Share.

game da Author