Kwalara:Dalibar makarantar kwana na mata dake Kawo Kaduna ta rasu 39 na kwance a asibiti

0

Jami’in hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) na jihar Kaduna Suleiman Ibrahim ya bayyana cewa cutar amai da gudawa ta yi sanadiyyar rasa ran wata dalibar makarantar kwana na mata ‘Government Girls Secondary School (GGSS)’ dake Kawo.

Ibrahim ya ce bayan dalibar da aka rasa akwai wasu 39 da suka kamu da cutar da duk suna kwance a asbitin gwamnati dake kawo.

Bayan haka kwamishinan kiwon lafiya na jihar, Jaafaru Sani a ziyarar da ya kai makarantar ya tabbatar da bullowar cutar a makarantar, sannan ya ce gwamnati ta kai wadanda ake zaton suna sun kamu da cutar asibiti.

Jaafaru ya kara da cewa zuwa yanzu an sallami dalibai 15 cikin sama da 30 dake kwance a asibitin.

A karshe ya jadda cewa gwamnati da hukumar makarantar sun mai da hankali wajen ganin an dakile yaduwar cutar da kuma samar da rigakafi domin gujewa faruwar irin haka.

Share.

game da Author