An sako matan da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari bayan an biya miliyoyin naira

0

Masu garkuwa da mutane sun sako matan auren da suka sace a kauyen Maganda dake karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna.

Masu garkuwan sun sako Murja Adamu da Sukaila Adamu matan wani mazaunin garin Maganda mai suna Adamu Makwalla bayan biyan naira miliyan 1.15 kudin fansa.

Wani cikin abokan Alhaji Makwalla, Mustapha ya sanar wa PREMIUM TIMES cewa sai da aka biya kudin fansa har naira miliyan daya sannan aka sako Murja ranar Asabar.

Haka ita ma Sukaila sai da aka kara wa masu garkuwan naira 150,000 sannan suka sako ta ranar Lahadi.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne wasu mahara suka kai hari Kauyen Maganda, da ke karamar hukumar Birnin Gwari hari sannan suka yi garkuwa da matan Alhaji Makwalla.

Bayanai sun nuna cewa maharan kan tsallako ne daga kauyukan Jihar zamfara idan za su aikata wannan mummunar aiki.

Share.

game da Author