Shugabannin bangaren Sabuwar PDP da ke cikin jam’iyyar gambiza ta APC, sun janye daga zaman sulhun da suke yi da gwamnatin Muhammadu Buhari.
A cikin wata takarda sa Shugaban na Sabuwar PDP, Kawu Baraje ya sa wa hannu, ta ce sun yanke shawarar janyewar ne biyo bayan irin halin bi-ta-da-kullin da ake yi wa mambobin APC da ke cikin bangaren su.
Baraje ya zargi Fadar Shugaban Kasa da yin baki-biyu da kuma harshen-damo.
Sannan kuma ya ce bangaren na su bai yi amanna da imanin riko da gaskiyar bangaren gwamnati ba dangane da yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin su.
Ya bayar da misalin irin gayyatar da aka yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki zuwa hedikwatar ‘yan sanda, inda aka danganta shi da fashi da makami.
Ya ce wannan daya ne daga cikin irin fuska-biyun da gwamnatin Najeriya ke nunawa, kuma hakan ya sa ita gwamnatin ba abar bai wa amana ba ce.
Su dai Sabuwar PDP, su ne wadanda jam’iyyar APC ta taka gadon bayan su har ta samu nasarar cin zabe a karkashin dan takara Muhammadu Buhari.
Buhari ya shafe zango uku ya na takara kuma ya na faduwa. Bai samu nasara ba sai da ya hada baki da Sabuwar PDP, wadanda suka balle daga cikin jam’iyyar PDP suka koma APC gab da zaben 2015.