Jami’in yada labarai na ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Adamawa Mohammed Abubakar ya bayyana cewa cutar kwalara ta yadu zuwa kananan hukumomi biyu a jihar.
Kananan hukumomin da suka harbu da cutar sun hada da Hong da Maiha.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne cutar kwalar ya bullo a kananan hukumomin Mubi ta Arewa da Mubu ta Kudu inda a kalla mutane 434 suka kamu da cutar sannan mutane 13 sun rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar. Bayan haka kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Charity Warigon ta bayyana cewa kungiyar za ta aika da ma’aikatan kiwon lafiya 39 zuwa kananan hukumomin Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu.
Amma sai gashi yau an wayi gari cutar ta yadu zuwa kananan hukomomin Hong da Maiha inda akalla mutane hudu sun kamu da cutar.
” Abubakar yace koda yake ba bu wanda ya rasa ran sa a kananan hukumomin.