Bincike ya nuna cewa yawan haihuwa na yi wa mace illa matuka musamman ga zuciyar ta.
Wasu likitoci da suka gudanar da bincike a jami’ar Cambridge sun gano haka a bincike da suka yi.
Jagoran binciken Clare Oliver – Williams ta bayyana cewa sun gudanar da bincike ne kan matan da suka haihu ya’ya biyar zuwa sama da matan da ‘ya’yan su da ko biyu.
” Binciken ya nuna mana cewa wadannan mata da suke da shekaru tsakanin 45 zuwa 64 na fama da matsalolin cututtukan dake kama zuciya.
Clare Oliver – Williams ta ceta roki mata da suyi rage yawan haihuwa saboda illolin dake tattare da haka musamman idan girma ya karato.
Discussion about this post