Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo na ganawa ta musamman da sufeto janar din ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris da shugaban hukumar DSS, Lawal Daura da ministan Shari’a Abubakar Malami a ofishin sa.
Wannan ganawa dai yana da nasaba da hayagagar da ke nemar ta dulmiyar da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kan zargin da ake masa na hannu dumu-dumu da yake dashi a ayyukan ta’addanci a jihar sa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince wa sufeto janar din ‘yan sanda Ibrahim Idris cewa idan har an sami shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da laifi a kamayamayar da ta dabaibaye shi na hannu da ake zargin sa da shi a ayyukan ta’addanci a jihar Kwara, doka ta hukunta shi.
Buhari ya bayyana haka a wasu bayanai da muka samu cewa lallai Idan har Saraki na da hannu a wadannan ayyukan ta’addanci da ake zargin sa da su a hukunta shi kawai.
An ga sufeto janar din ‘yan sandan kasa Ibrahim Idris a fadar shugaban kasa dauke da damin takardu ya nufi ofishin shugaban kasa.
Sahihan rahotannin da muka jiyo, sun nuna cewa tabbas Idris ya taho ya nemi izini ne a wajen shugaba Buhari da sanar masa irin abubuwan da suka gano a binciken fashin da akayi a bankunan garin Offa dake jihar Kwara.
Wasu daga cikin ‘yan fashin sun shaida wa jami’an tsaro cewa shugaban majalisa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed ne ke basu kudade da makamai sannan da wadata su da kayan aiki domin aikata ayyukan tsafe-tsafe da ta’addanci a jihar.
Idan ba a manta ba tun kafin a kai ga haka Saraki ya yi shelar cewa akwai barazanar yi masa kazafi da ake shirin yi na danganta shi da ayyukan matsafa da ta’addanci a jihar da ‘yan sanda ke kokarin yi masa.
A halin da ake ciki Saraki na cikin tsaka mai wuya domin kuwa rundunar ‘yan sanda za su iya kama shi ya fuskanci hukunci duk da shine shugaban majalisar dattawa, domin kuwa doka bata bashi wannan kariya ba.
Masu sharhi dai sun ce wadannan duk jagaliyar siyace, farautar sa ake yi yanzu kuma babu makawa idan bai yi a sannu-sannu ba zai fada tarkon da aka dana masa.
Shi ko gwamna Abdulfatah yana da cikakkiyar kariya, ba za a iya ci masa mutunci ba muddun ya na wannan kujera na gwamnan jiha.
‘Yan fashin dai sun mika makamai har da mota dauke da lambar Saraki wai dasu suke sharholiyar su da ayyukan su na ta’addanci a fadin jihar, sannan su dama can a karakashin ikon Saraki suke da gwamnan jihar.