JA FADO JA YA DAUKA: Yadda harkalla, ’yan-ci-ka-ware suka gurgunta ” Shirin Noman Shinkafa na Gwamnatin Tarayya”

0

MATASHIYA

“Shugaba Muhammadu Buhari ya kudiri aniyar narka makudan kudade a fannin inganta noma, ta yadda za a samar wa jama’a ayyukan yi a yankunan karkara.

“ Ina kuma da tabbatacin cewa an samu gagarimar nasara a wannan fanni, domin miliyoyi sun samu ayyukan yi a fannin noma.

“Shugaban Kasa da kan sa ya shaida min cewa a da can baya mutanen kauyen su su kan bayar da gonakin su jingina ga manoma daga Kano. Amma yanzu kowa ya koma gona.

“Wani abin sha’awa ma shi ne, baya ga yadda a yanzu manoma ke ta tururuwar zuwa aikin Hajji, a gefe daya kuma su na ta takarar kara aure.”

Osinbajo ya yi wannan jawabi ne a wurin taron Lacca na Bola Tinubu, cikin watan Maris, a jihar Legas.

Sai dai kuma wani abin da dimbin masu sauraren Osinbajo ba su sani ba, shi ne, mafi yawan wadanda Osinbajo ya ce sun kara aure, kuma sun biya kudin aikin Hajji, to ba fa da ribar noman shinkafar da suka samu ne suka gabji kudade suka biya bukatun na su ba.

Mafiya yawa sun je Hajji kuma sun kara auren ne daga cikin madarar kudaden da aka ba su lamuni domin a karfafa musu yin noma a karkashin Shirin Gwamnati na bai wa Manoma Lamuni, da aka fi sani da ‘Anchor Borrowers’ Programme.

Wani kwakwaran bincike da PREMIUM TIMES da kuma wani Bugun-hisabin Gwamnatin Buhari mai suna ‘Buharimeter’ da aka gudanar a cikin jihohi biyar, Legas, Ekiti, Kebbi Kaduna da Ebonyi – da kuma cikin Jamhuriyar Benin, ya nuna cewa ba a haifi shirin da kafafu masu karfin da za su iya daukar sa ba, dalili kenan tuni ya gurgunce.

Shirin ya samu nakasu bayan da gwamnati ta rabas da naira har bilyan 55 a matsayin lamuni ga manoma domin inganta amfanin gona har Najeriya ta rika ciyar da kan ta, ta yadda ba sai an shigo da shinkafa daga waje ba.

JA YA FADO JA YA DAUKA

Shirin ya kara fito da mafusatan manoma wadanda suka yi kukan cewa ‘yan siyasa ne suka kwace harkar rabon kudin lamunin noman, suka rika bai wa manoman bogi ramcen kudaden, wadanda yawancin su ma ko gona ba su taba shiga ba.

Sun yi korafin cewa wadannan ‘yan siyasar karkara sun rika yi wa ‘yan barandar siyasar su hasafin kudin ramcen, a matsayin ladar wahalar dawainiyar da suka yi musu a lokacin da ake yakin neman zabe. Binciken da muka gudanar ne ya tabbatar da haka.

Bincike ya nuna yadda aka rika maida kungiyoyin manoma saniyar-ware a lokacin da ake raba kudaden lamunin noman.

Har ila yau, wani bincike da PREMUM TIMES da BUHARIMETER suka gadanar, ya tabbatar da cewa muradin gwamnati na ganin Najeriya ta zama mai iya ciyar da kan ta da shinkafa, ta hanyar noman shinkafa, abin duk ya zama tatsunita, domin har yanzu ana ruguguwar yin sumogal na shinkafa daga Jamhuriyar Benin.

SHIRIN BADA LAMUNIN NOMAN SHINKAFA

Duk da irin yadda Buhari ya yi wa al’umma jawabin kudirin sa na ganin an inganta noman shinkafa, da hudubar da ya rika yi wajen nuna muhimmancin dogaro da noma a na cikin gida, duk wannan bai shiga kunnuwan dimbin jami’an lura da shirin ba da kuma da yawan wadanda suka karbi lamunin kudaden.

Wace matsala aka samu? Harkalla, son rai, arcewa da kudin bashin na bilyoyin nairori da kuma almundahana iri daban-daban.

An kuma yi kwakkwaran zargin yadda aka rika karkatar da kudaden.

YA SHIRIN BADA LAMUNIN NOMA YA KE?

Shirin wanda aka fi sani da Anchor Borrowers, ya na bada kayan iri da kuma ramcen kudade ga manoma wadanda kanana ne, domin su habbaka noman shinkafa, musammam don a daina dogaro da shinkafar waje.

An tsara cewa idan manomi ya noma shinkafar, zai saida ta ne ga jami’an shirin Bada Ramcen, inda za a zuba musu kudaden su a asusun ajiyar da aka sa kowa ya bude a banki.

Wasu amfanin gonar da kuma aka karfafa nomawa sun hada da shinkafa, masara, alkama, auduga, rage, tumatir da kiwon dabbobi.

Amma sai aka fi karkafa noma shinkafa, aka rika damfara kudade ga manoma da sunan ramce, a kan kowa zai bayar da kudin-ruwa har kashi 9 bisa 100 na uwar kudin da ya karba.

YADDA AKA TSARA RABA WA MANOMA KUDADEN

Duk manoman da ke bukatar karbar ramcen kudaden sun rika kafa kungiya-kungiya ta manoma.

Sunn rika nuna shaidar cewa sun mallaki gonaki, kuma su na jimirin yin noman.

An bukaci kowanen su ya bude asusun ajiyar banki, tare da mallakar lambar tantance asusun ajiya ta BVN.

An tsoma jihohi a cikin batun sa’ido kan wadanda aka bai wa ramcen noma, ta hanyar neman su kafa Kotunan Musamman Kan Manoman da suka ci lamunin suka ki biya.

TSUNTSU DAGA SAMA GASASSHE

Shirin da gwamnati ta yi da kyakkyawar niyya ya fada hannun ‘yan-cha-buros, wadanda watanni shida bayan da Buhari ya kaddamar da shirin, an rasa inda kudin suka yi. Ba kudi, babu iri, babu noma kuma ba a daina fasa-kwaurin shinkafa ba. Lokacin Da aka fara kaddamar da shirin kuma sai aka yi fatali da dukkan ka’dojin da aka gindaya wa wadanda aka ce sai su za a bayar wa bashin.

“Manoma fa suka fara karbar lamuni, kawai suka rika kallon kudin a matsayin su ma rabon su ne daga cikin baitilmalin Najeriya, aka kawo musu har gida.

“Akwai ma wasu shugabannin kananan hukumomin da suka rika ce wa manoman kada ma su rika fargaba don kudaden sun salwanta a hannun su kuma ga shi babu alamar shuka balle noma a cikin gonakin su.” Haka Segun Atho, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Atho ya ci gaba da bayyana wa PREMIUM TIMES cewa akasarin wadanda aka bai wa lamunin ko rike fartanya ma ba su iya ba, duk ‘yan jagaliyar siyasa ne.

WALA-WALAR DA AKA YI WA MANOMAN KEBBI

Idan ka hau babur din acaba tun daga Kogin Jega har zuwa Aliero da Karamar Hukumar Jega, wani mai nuna wa PREMIUM TIMES hanya ya na ta nanata yadda yadda aka yi watsi da manoma na gaskiya, aka rika ba ‘yan bulkara bashi kudi a hannu, ba ma a banki ba.

“An rika raba bashin ga wadanda ba manoma ba, ba su ma san yadda ake noma ba kuma kudi aka rika dumbuzowa ana ba su, gar-da-gar.

Shugaban Karamar Hukuma zai zo ya ce nasa mutanen ba su samu ba, shi ma dan majalisa zai zo ya ce ina na mutanen sa? Haka Sanatoci da ’yan majalisar tarayya. To ya za ka yi da irin wannan?

Mutumin ya bai wa wakilin PREMIUM TIMES dariya a lokacin da ya ce “A Jega fa sai da aka gama yin watandar kudaden karkaf sannan aka dawo ana safiyon banza da wofi, da sunan duba gonakin manoma. Kawai aka raina wa gwamnati wayau don a ce wai sai da aka tantance sannan aka yi watandar.”

Daga cikin manoma goma da PREMIUM TIMES ta zanta da su a jihar Kebbi, babu wanda ya ce an ba shi lamunin.

Sa’idu Usman ya nuna wa PREMIUM TIMES gonar sa a cikin takaici cike da fuskar sa. Ga dai shinkafa ta fito sosai amma kuma rashin ruwa ya sa ta yi ja da kuma ruwan dorawa, ta kamo hanyar bushewa, saboda ba hi da kudin da zai sayi injin banruwa domin ya rika jawo masa ruwan da zai rika sheka wa shinkafar.

Rice farm

“Ni dai ba ni ga tsuntsu kuma ba ni ga tarko. Ban samu komai daga gwamnati ba. Ba injin banruwa, ba bututun jawo ruwa, ba iri, ba a ba ni komai ba. Da kudi na na sayo komai. Maleji kawai na ke yi, domin matsawar babu tallafi daga gwamnati to manomi ba abin da zai iya yi, sai dai walahar banza kawai.”

MANOMA SUN GUDU SUN BAR LADAR SU

“Manoma da yawa sun gudu sun bar gonakin su saboda wahala. Ga shi nan dai ka na gani da idon ka.”

“Haushi ba zai kama ka ba, sai ka je Kebbi ga motocin tarakta nan na noma ajiye, an ki raba wa manoma, kai sai ka rasa abin da za a yi da su.”

Muhammad Gulma, wani dan jarida da ya koma manomi, ya shaida min yadda jami’an gwamnatin jihar Kebbi ke kin bayar da rajista ga duk wanda bai ba su cin hanci ba.

“Batun bashi fa? “Duk sun ci bilis, ba biya za su yi ba, tunda dama can ba manoma ba ne. Gwamnatin Kebbi ta raba wadanda ta ga dama. Na cika fam, amma ba a ba ni ba, sai ka bayar da cin hancin naira 50,000. Ban bayar ba, shi ya sa ban samu ba.”

ALHERI YA ZAMA SHARRI A KADUNA

A Jihar Kaduna kuwa, shirin bada rance ga manoma ya zama sharri. Tashin farko, ba a raba wa manoma kudaden da kayan noman ba har sai bayan da lokacin noma wuce. Shi ya sa akasarin abin da suka shuka bai yi yabanya ba.

Yawancin wadanda aka bai wa bashin, duk an ba su ne ladar gumin da suka yi wajen zaben Buhari. Kuma babu ruwan su da tunanin akwai ranar da za su biya, domin ba su san wannan ranar ba.

Wani jami’in FEHCON a Kaduna mai suna Abdul-Rahman Musa, ya ce shirin noman a Kaduna kashi 80 bisa 100 bai yi nasara ba.

“Saboda ba a dauki matakin da zai sa shirin ya samu nasara ba, son rai aka yi da kuma son ran ‘yan siyasa. Kawai dai wasu ‘yan ragabza sun samu hanyoyin da suka azurta kan su da rana tsaka, ba tare da sun yi gumi sun yarfe ba.”

HARIGIDON KUNGIYAR AGBEREMI A EKITI

Manoman a jihar Ekiti sun ga takaici, domin wasu gungun ma’aikatan gwamnati har su 357 ne suka kafa kafa kungiya, mai suna ‘Agberemi’ aka shigar da su a cikin shirin noma.

Aka bai wa kowane daga cikin su ekar gona da nufin su noma a yankin Oke Ako. Ba a ba su kudade ba, amma ga gonaki an ba kowa.

Cikin 2016, Ministan Gona Audu Ogbe ya kai ziyara, har ya jinjina wa shirin na ‘Agberemi.’

Audu-Ogbeh

Bayan buki da taro ya watse, sai aka bar manoman ‘Agberemi’ cikin fargaba: Na farko dai sun fara noma a makare, sai cikin Yuli zuwa Agusta suka fara shuga ko dashen iri.

Kowanen su ya san ba lallai ba ne yabanyar sa ta kai labari. Suka rika kwana addu’ar rokon ruwa ya ci gaba da zubowa har Disamba.

Sun samu ruwan kamar yadda suka yi ta addu’a, amma sai ya dauke gaba daya a cikin watan Oktoba. Kuma daidai lokacin ne amfani gonar su ya fara kosawa, ya ke bukatar ruwa fiye da kowane lokaci.

Ba su sake samun ruwa ba har sai Disamba. Ya zuwa lokacin kuwa, sun rigaya sun fitar da rai cewa sun dibga asara kawai.

Daya daga cikin manoman, Tai Komolafe, wanda Darakta ne a Ma’aikatar Gona ta Jihar Ekiti, ya bayyana wa PREMIUM cewa sun dibga gagarimar asara, sai dai gyaran Allah kawai.

Kuma an bar su da biyan bashin naira milyan 60.

YADDA AKA RABA LALATACCEN TAKI DA IRI A EBONYI

Shugaban Kungiyar Manoma na Jihar Ebonyi Livinus Okoh, ya shaida wa Premium Times cewa su dai irin shinkafar da aka ba su tilas ta sa suka maida shi, domin ya ki kamawa saboda lalatacce ne, kuma dama a makare a raba musu shi, bayan lokacin dashe ya wuce.

Ya ce kuma takin zamanin da aka raba musu shi ma lalatacce ne, saboda an ba su shi ne lokacin da ka’idar daina aiki da shi ta zo daidai.

“To an ba mu takin zamanin da a rubuce zai daina aiki a cikin watan Yuni alhali mu kuma za mu fara aiki da shi a cikin Yuli.” Ka ga an yi, ba a yi ba kenan.

BATALIYAR SUMOGAL DIN SHINKAFA

Yayin da Shirin Noman Shinkafa na ABP ya gurgunce dalilin matsalolin da muka bayyana a sama, can kuma a Kudu maso yammacin Najeriya, kan iyakar kasar da Jamhuriyar Beni, an bude wata kasaitacciyar bataliar sumogal din shinkafa ‘yan Thailanda har ma da ‘yar Vietnam, fiye da yadda ma ake yi kafin a haramta shigo da su.

Haka ma a kan iyakar Seme da Jamhuriyar Nijar, sumogal ya ragu, amma kuma an bude wata sabuwar bataliyar sumogal a Owode-Apa, yamma da Badagry.

Gaba dayan mutanen garin ko kuma a ce mazauna wurin sana’ar fasa-kwauri ce kawai su ka maida hankali a kai. Ga manyan motocin da ake wa sokale, ana loda wa wasu, ga kananan motoci wadanda ake cire wa kujeru kuma ana kara fafare su domin su rika cin buhunan shinkafa da yawa.

Tsakanin sabon dandalin fasa-kwauri zuwa kan iyakar Seme akwai wurn da jami’an tsaro ke bincikke har kusan sama da 50. Amma duk ihun-ka-banza ne.

Amma duk da haka, bai hana jami’an kwastan su na bin motocin dakon shinkafar sumogal a cikin Najrriya a guje su na bude musu wuta ba. Ko da kuwa bugu biyar ne direba ya dauko.

Bisa kwakkwaran alamu dai naira bilyan 55 da Gwmnatin Buhari ta raba wa manoma bashi, ta bi shanun-sarki kenan, babu mai iya cewa a dawo da su.

Ko ba komai, ‘yan siyasar karkara da ‘yan jagaliyar da aka raba wa, su na da bakin cewa ‘ladar askin’ da su ka yi wa APC a zaben 2015 ce su ka ci.

Share.

game da Author