Rundunar ‘Yan sanda ta gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da ya bayyana domin amsa tambayoyi dangane zargin alakar da ke tsakanin sa da wasu ‘yan fashin da suka yi kisa a bankin garin Offa, cikin Jihar Kwara, watanni biyu da suka gabata.
Kakakin jami’an tsaron mai suna Mosheed Jimoh ya bayayyana haka yau, a Abuja.
Jimoh yace an kama mutane 22 da ake zargi da yin fashin, wanda ya afku a ranar 5 Ga Afrilu, a garin Offa, inda aka kashe mutane 33, cikin su kuwa har da ‘yan sanda tara.
Wadanda aka kama din sun bayyana wa ‘yan sanda matukar kusancin su da Sanata Bukola Saraki.
Cikin wadanda aka kama din akwai manyan gogarman fashi biyar da suka hada da: Ayoade Akinnibosun, Ibukunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salawudeen Azeez, Niyi Ogundiran da kuma wasu 17, wadanda suka yi fashin banki a Offa sannan suka kashe mutane 33, ciki har da ‘yan sanda 9.
An yi sanarwar gayyatar Saraki makonni uku bayan an dauke wasu da ake zargi daga Ilorin, babban birnin jihar Kwara, aka maida su Abuja domin bincike.
Tun a lokacin dama Saraki ya yi saurin yin sanarwa cewa ‘yan sanda na neman su goga masa kashin-kaji ne.
Sai dai kuma ‘yan sandan sun ce sam ba haka ba ne, kuma suka gargade shi da ya guji tsoma bakin sa a harkokin da suka shafi masu aikata munanan laifuka.
Jawabin da rundanar ‘yan sanda ta fitar yau Lahadi, ta ce wadanda ake zargin duk sun amsa cewa ‘yan bangar siyasar Bukola Saraki ne da kuma Gwamna Abdulfatah Ahmed.
A ranar da aka yi fashin dai sai da suka dira bankuna har shida a garin, da suka hada da: (i) First Bank Offa (ii) Guarantee Trust Bank Offa (iii) ECO Bank Offa (iv) Zenith Bank Offa (v) Union Bank Offa (vi) Ibolo Micro Finance Bank Offa da kuma (vii) Hedikwatar Dibijin na ‘Yan sanda da ke Offa.
Sun kwashe miliyoyin kudade, kuma suka gudu da bindigogin ‘yan sanda samfurin AK 47 har guda 21.
Sun ce Saraki ne da Gwamna Abdulfatah ke daukar nauyin su ta hanyar ba su kudade da kuma ba su makamai da motocin zirga-zirga.
An ce an samu babban gogarman ‘yan fashin mai suna Ayeode Akinnibosun na amfani da wata kartsetsiyar mota kirar LEXUS JEEP, wadda ya manna wa sunan “SARAKI”.

Bincike ya nuna cewa an yi fashi da motar kuma a ranar 16 Ga Mayu sai aka shiga da motar, wadda launin toka gare ta, aka baye ta cikiin gidan gwamnatin jihar kwara, aka cire sunan “Saraki”, aka maida lamba: KMA 143 RM mai dauke da rajistar sunan Ayoade Akinnibosun.
Daga baya an samu motar acikin harabar Ma’aikkatar Muhalli da Kula da Gandun Daji, ita kuma lamba mai lakabin “SARAKI” aka same ta a hannun wani mai suna Adeola Omiyale kuma dama shi ne aka ce ya tuka motar ya kai ta cikin gidan gwamnati bayan da aka yi fashin.
An kuma ce daya daga cikin mukarraban gwamnan ne ya ce a maida motar a ajiye a Gidan Gwamnati, saboda shi ma ya na sane da fashin.
‘Yan sanda sun ce shi ma Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnatin Jihar Kwara ya na sane da fashin. An kama shi, kuma shi ne ya shirya yadda za a cire sunan “SARAKI” a jikin motar shi ne kuma ya yi mata rajista da sunan Ayoade Akinnibosun, babban gogarman fashin.
Ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfabar da wadanda ake tuhuma da kuma kama duk sauran masu hannu.
WADANDA AKE ZARGI
I. Ayoade Akinnibosun
ii. Ibukunle Ogunleye
iii. Adeola Abraham ‘
iv. Salawudeen Azeez ‘
v. Niyi Ogundiran ‘
vi. Michael Adikwu
vii. Kabiru Afolabi
viii. Omoseni Kassim
ix. Kayode Opadokun
x. Kazeem Abdulrasheed xi.
xii. Adewale Popoola
xiii. Adetoyese Muftau
xiv. Alexander Reuben
xv. Richard Buba Terry
xvi. Peter Jasper Kuunfa
xvii. Ikechukwu Ebuka Nnaji
xviii. Moses Godwin
xix. Adeola omiyale
xx. Femi Idowu
xxi. Alabi Olalekan
xxii. Yusuf Abdulwahab EXHIBITS
Discussion about this post