Tsakanin Malamai da Shugabanni; Wanene matsalar Al’umma? – Daga Magajin Malam

0

Rashin cikkaken fahimtar Addini shine babban matsalar Al-Ummar mu amma har yanzu ba mu gane ba ballantana mu zurfafa ilimin Addini.

Za ka ji mutane su na cewa: idan aibanta shugaba bai halatta ba, to aibanta Malami ya halatta ne?

Wannan tambayar kawai ta tabbtar da karancin fahimtar Addininsu a fili.

Abunda ba su sani ba shine:

#Mugun Shugaba kokoluwar abunda zai bata maka shine jin dadin rayuwarka ta duniya. Kuma duk lalacewarsa yafi ace babu shi kwata-kwata, domin idan babu shugaba zaman gidanka ma ba zai yiwu maka ba ballanta fita waje, saboda kowa zai zama hukuma: mai karfi ya danne mara karfi, masu yawa su danne marasa yawa, mai kudi ya danne mara kudi, dss.

Da wannan ne Shari’a ta wajabta ma mabiya yin biyayya ga shugaba saboda an wakilta umurni da hani a hannunsa.

Saboda haka ne ma Manzon Allah (SAW) ya yi ma Sahabansa wasici da yin biyayya ga shugaba ko da kuwa bakin bawa ne Dan Habasha aka shugabantar da shi akansu, wannan misali ne na karfafa mahimmanci biyaya ga shugaba, lura da yadda Larabawa a jahiliya suke kyaman bakin mutum ballanta kuma ace bawa ne.

Sahabai (RA) ba’a taba samun dayan su da aibanta shugaba ba ballanta yi masa bore ko tawaye, duk da cewa mafi yawan su sun ga zamanin shugabanni daban-daban: Abubakar, Umar, Uthman, Ali, da Mu’awiyah (RA) dss. Tsakaninsu da shugabanni sai biyayya da Addu’ar Allah ya datar da su da abunda Yake so kuma Ya yarda da shi, domin jarabawa ce Allah Ya kaddara musu na yin shugabanci, wanda yi musu fatan alheri da dacewa da cin jaraba yana daya daga cikin hakkokinsu akan yan uwansu Musulmai. Yi musu bore da mugunyar Addu’a saba ma Allah ne da Manzonsa (SAW) da toye hakkin yan uwantaka na Musulunci wanda suke kawo fitintinu a cikin Al-Ummah.

Daya daga cikin magabata nagari yace: Da Allah zai yi masa alkawarin amsa masa Addu’arsa guda daya tak, to da zai yi ma shugaba ne ita na nema masa shiriyar Allah, domin idan ya shiryu Al-Ummah za ta shiryu.”

#Shi ko mugun Malami mugun makami ne wanda zai bata maka duniyarka da Lahira. Kamar yadda Manzon Allah ya fadi: “mugun Malami yana yin muguwar fatawa, ya bata ya batar…” Domin gama-garin mutum za su daukeshi a matsayin hujja na Addini. Idan Malami ya bi Allah da Manzonsa (SAW) ya kubuta ya kubutar da mutane, idan kuma mugu ne ya bi son zuciyarsa ya halaka ya halakar da mutane. Shiyasa ya zama wajibi a fadakar da mutane mugun Malami.

Hawa mumbarin mugun Malami ya fadi laifin shugaba da aibanta shi, koyad da mabiya mugun tunani da tasirantuwa da shi ne, sabanin yi ma shugaba Addu’a ta shiriya da samun nasara saboda mabiya su koya su tasirantu da hakan. Wannan ke nuna cewa Malami kodai ya zama mai koyad da Al-Ummah alheri ko sharri daga maganganunsa akan mumbari ko majalisin karatu.

Idan Malami nagari ne mai Ikhlasi da neman maslaha ma Al-Ummah kuma ba makwadaici ba, kamata ya yi ya je ya yi ma shugaba Nasihah a sirrance ba koya ma mutane aibanta shugaba akan mumbari ba. Idan Malami mai Ikhlasi ne kuma ba mai kwadayi ba, to shugaba komai tsaurin kansa sai ya saurare shi. Fir’auna ma ya saurari Annabi Musa (AS) duk da cewa yana zarginsa da yi masa butulci saboda shi ya raineshi.

Kamar yadda naga an hikayo a shafin facebook cewa: Tsohon Shugaban Kasa Shagari yace: a zamanin mulkinsa duk lokacin da ya je hutu Sokoto, idan aka ce masa ga Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (rh) ya zo wurinsa sai gabansa ya fadi, saboda yana yi masa Nasihah akan hakkin da aka daura masa na Amanar Al-Ummah wanda yake saka jikinsa ya yi sanyi. Idan Sheikh Gumi zai tafi ya kawo kyautan kudi ya bashi baya karba.

Wani zai ce ai shugabannin mu na yanzu basa daukan Nasihah kuma kamar Addu’ar shiriya bata tasiri akan su, to matsalar mu ne, domin “kamar yadda kuke haka za’a shugabantar akan ku”. Shugaban nan dai daga cikinmu yake ba daga wani wuri ba. Mafita sai mun gyara, mun yi hakuri kuma mun tsananta Addu’a ba yin bore da tawaye ba.

Mugun Malami hadarinsa tafi ta mugun dan siyasa, domin tasa (dan siyasa) ta duniya ce, takaitacciya ta dan wani lokaci ne a duniyar ma. Fitinar Boko Haram wanda har yanzu ba mu gama fita daga cikinta ba tasirin mugun Malami ne. Duk wanda ya bibiyi yadda Kungiyar Boko Haram ta fara har zuwa inda ta kai, ya tabbata masa cewa daga irin wannan aibanta shugabanni ta fara, na fadan aibunsu da kiransu tagutai a gaban mabiya, har ta kai ga yin bore da daukan makami don su kafa daula tasu ta daidai da adalci. Mun ga irin musifar da yakin wannan kasar ya shiga a sakamakon tasirin wa’azin muyagun Malamai yan Boko Haram, sun bata ma mabiyansu duniyarsu da Lahirarsu, kuma suka haddasa halaka rayukan dubban Jama’a da dukiyoyinsu. Irinsa ne muka sake gani wurin Zakzaky da mabiyansa.

Su ma wadancan ma su shiga rigan malamta suna tuzura Jama’a akan mahukunta, da za su ware su ce za su yi fito-na-fito da Hukuma za’a a sami mabiyan da za su bi su a haifar da fitina da tada zaune tsaye a cikin Al-Ummah.

Kasashe irin su Libya da sauransu da irin wannan mugun wa’azin muyagun Malamai akan mahukunta ne har su ma suka kai halin da suke cikin a yau. Yanzu su gwammace da sun yi hakuri da yin Adduar shiriya ga shugabannin da suka yi ma bore da tawaye da yafi musu.

Bisa wannan ne muka ga ya zama mana wajibi mu fadakar da Al-Ummah mugun Malami dake tunzura Jama’a akan mahukunta wanda yake kai ga haddasa fitina da musifu a cikin kasa.

Wannan shine gaskiyar lamari kuma shine Mazhabar da ni da ire-ire na muke akai na yadda danganta tsakanin shugaba da mabiya yake a mahangan Musulunci da kuma yadda Shari’a ta tsara mu’amalar bangare biyun ya zama.

Wanda ya gamsu Alhamdu lillahi, wanda kuma bai gamsu ba to Allah ya ganar da shi. Mu dai ba za mu fasa yin Nasihah akan yin hakuri da mahukunta da yin Addu’a tagari a gare su ba. Idan kuma wani hakan bai masa ba, to sai ya bar bibiyar mu a wannan kafa ta sada zumunta, illa iyaka kenan

Allah muke roko Ya shiryar da mu da shugabannin mu Ya datar da su, kuma Ya shiryad da masu son tada fitina a cikin Al-Ummah, in kuma ba masu shiryuwa ba ne Ya iyam mana sharrinsu, ameen

Magajin Mallam: Abu Yahya (Aslam)

Mun sami wannan nasiha ne daga shafin sada zumunta na Magajin Malam.

Share.

game da Author