Jami’in shirin Fadama III Tayo Adewumi ya bayyana cewa za su tallafawa ‘yan gudun hijira maza da mata 1,840 a jihar Bauchi.
Adewumi yace Fadama III zai tallafa wa ‘yan gudun hijiran ne ta hanyar wani shiri da ya tsara mai taken ‘Community Action Plan (CAP)’.
Ya sanar da haka ne ranar Juma’a a taron kadamar da sabuwar tsarin ‘FADAMA VANGUARD’da aka yi a Bauchi.
“A shekarar bara tsarin ya tallafa wa mutane 22,551 wanda kashi 53 bisa 100 na yawan mutane mata ne sannan daga cikin su muka raba wa mutane 2680 kayan abinci.
” A Bana kuwa zamu tallafa wa mutane 1,840 da kayan abinci, koyar dasu sana’o’in hannu, noma da sauran su domin inganta su.”
A karshe ya ce za su dauki ‘yan gudun hijiran aiki a matsayin ma’aikatan da za su shuka itatuwa, shara da gyara garuruwan da Boko Haram suka kona saboda mazauna wadannan garuruwa su koma matsugunin su.
Discussion about this post