BARAKA A APC: Bangaren APC ta kacaccale a Kaduna

0

Bangaren APC dake adawa da gwamnatin jihar Kaduna a da bangaren jam’iyyar dake muradin gwamnati mai ci a jihar mai suna APC Restoration ta kacaccale zuwa gida biyu.

Ita dai ‘APC Restoration’ tana karkashin shugabancin Tijjani Ramalan da wasu ke ganin sanata Suleiman Hunkuyi na da ga cikin masu daure mata baya a jihar.

Barakar da aka samu kuwa shine na wasu daga cikin mambobin kungiyar sun zame kansu inda suke zargin jagororin kungiyar da kaucewa daga makasudin kafa kungiyar.

Hasalallun ‘yan kungiyar sun nada sabon shugaba da sakatare.

An nada Awwal Fatoki a matsayin shugaban kungiyar da Mohammed Molash a matsayin sakataren kungiyar.

Da yake fadin dalilan da ya sa suka kafa bangare sabuwa na kungiyar, Fatoki ya ce ba za su iya ci gaba da zama karkashin shugabancin Tijjani Ramalan ba.

” Ga ba daya kungiyar APC Restoration din ya karakata daga ainihin manufofin kafata. Mai makon a maida hankali wajen mara wa gwamnati mai ci baya domin ci gaban jihar, sai aka sa son rai aka mai da abin siyasa ana muzguna wa gwamnati da kushe ayyukan ci gaba da take yi a jihar.

” Dalilin haka muka ga ba za mu iya ci gaba da zama karakashin irin wannan shugabanci ba muka kafa tamu.”

Idan ba a manta ba, dama can jam’iyyar ta rarrabu har gida uku ne a Kaduna. Akwai APC Akida, APC na asali, ‘APC Restoration’ sannan yanzu kuma ‘APC Restoration na biyu’.

Share.

game da Author