Shugaban jam’iyyar APC John Oyegun ya fadi cewa ba zai fito takarar shugabancin jam’iyyar APC a zaben jam’iyyar mai zuwa.
Oyegun ya bayyana haka ne da nuna rashin jin dadin sa ga yadda jam’iyyar take neman ta dulmuye cikin tabun da yake kokarin shanye ta da kata-kata, da rashi jituwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
“Ina da damar tsayawa takara nima a matsayina na shugaban jam’iyyar da ya shugabanci jam’iyyar ta kai ga ci a 2015.
” Na fi kowa sanin matsalolin jam’iyyar da irin hanyoyin da za a iya bi don shawo kan su. Amma don a zauna lafiya sannan da shawarwari da nayi na yanke hukuncin hakura da yin takara.
Yanzu dai ya nuna karara cewa tsohon gwamna, Adams Oshimhole ne dan takara tilo da ke neman wannan kujera. Dama kuma shine dan lelen Buhari.