HATTARA: Wasu bankuna fa sun fara durkushewa -Magu

0

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya bayyana cewa wasu bankunan kasar nan fa duk sun durkushe, saboda matsalar yadda ‘yan harkalla suka yi kaka-gida a cikin harkokin bankunan.

Magu ya ci gaba da cewa ya na so bankunan su gabatar da sunayen duk wani dan harkallar da ya ke da barankyankyama a bankuna.

Cikin wani bayani da kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya ce Magu ya hori bankuna da su rika bai wa EFCC bayanan da suka wajaba wajen taimaka wa hukumar ta na gudanar da ayyyukan ta yadda ya dace.

Ya ce batagari sun damalmala harkar bankuna, ta yadda wasu bankunan sun ma kusan zama fanko ko kuma kangon gini kawai.

Share.

game da Author