Mutane miliyan 17 suka yi gudun hijira daga Afrika cikin 2017- UN

0

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa akalla ‘yan Afrika miliyan 17 ne suka yi gudun hijira zuwa ta wasu nahiyoyin daban a cikin 2017.

Rahoton ya ci gaba da cewa wasu milyan 5.5 kuma sunn kwararo cikin Afrika daga wata nahiyar, yayin da wasu miliyan 19 ‘yan Afrika sun yi hijirar cikin gida daga nan zuwa can a cikin Afrika.

Hukuma Mai Kula da Kasuwanci Da Ci Gaban Afrika ta Malajisar, ta ce yawancin kaurar da jama’a ke yi a cikin Afrika, su na yi ne domin kokarin inganta rayuwar su, wadda hakan ke kara inganta tattalin arzikin nahiyar.

Sannan ya kara da cewa wadanda ke tsallaka kan iyakar wata kasa su fice neman rufin asiri, idan suka yi hakan rayuwar su kan kara inganta fiye da irin halin da su ke ciki a baya.

Babban Sakataren Kungiyar ne mai suna Mukhisa Kituyi ya bayyana haka.

Share.

game da Author