Kotu ta daure saurayin da ya sace wa budurwar sa waya da kudi

0

Kotu a unguwar Karmo, Abuja ta yanke wa wani saurayi hukuncin zama a kurkuku a dalilin zargin sa da laifin sace wa buduwar sa kudi da waya.

Kotun ta yanke wa Elvis Anthony mai shekaru 34 dake zama a Aso Pada a Mararaba jihar Nasarawa hukuncin haka ne ranar Laraba.

Ifeoma Ukahga lauyan budurawar Elvis mai suna Ene Ugah ta bayyana a kotun cewa Ene ta shigar da karar satan da Elvis ya yi mata ne a ranar 20 ga watan Faburailu a ofishin ‘yan sandan dake Utako.

” Ene ta bayyana cewa Elvis ya sace mata Naira 240,000 da wayar ta bayan sun dawo daga kasuwa da suka tafi tare da saurayin nata.

” Ta ce kudi da wayar sun bace ne jim kadan bayan Elvis ya fice daga gidan na ta, sannan tun daga wannan rana bata sake ganin Elvis ba sai da ‘yan sanda suka kamo shi.”

Elvis ya roki kotu da ta sassauta masa cewa ya tuba. An ba da belin sa kan naira 5000, ko zaman wakafi na wata biyar.

Share.

game da Author