Dalilan da ya sa za mu rusa gidajen Otel 47 a Maiduguri – Kaka Shehu

0

Kwamishinan shari’a, kuma Antoni Janara na jihar Barno Kaka Shehu Lawan ya bayyana wasu dalilai da ya sa gwwamnatin jihar zata rusa gidajen Otel 47 dake wasu unguwannin Maiduguri.

Idan ba a manta ba, mun ruwaito muku cewa da yawa dadgcikin mazauna garin Maiduguri sun yaba wa gwamnatin jihar game da shirin haka.

Kaka Shehu ya ce dole gwamnati ta dauki wannan mataki cikin gaggawa ganin cewa wuraren sun zamo matattarar ‘yan iska, mashaya, da karuwai.

Ma su wadannan Otel din sun zargi gwamnati da yi musu shigan bazata cewa ba a basu isasshen lokaci ba.

” Wurare kamar rukunin gidaje masu saukin kudi dake titin Baga, da Galadima sun fi zama unguwannin dake tada wa mutane hankali. A wadannan wurare akwai kananan Otel da dakunan Karuwai masu arha. Sannan matattara ce da mashaya muggan kwayoyi da baje kolin su babu mai ce musu uffan.

” A nan ne wata daliban jami’ar Maiduguri ta rasa ranta inda saboda kishi wani saurayinta ya kwara mata asid. Kuma a nan unguwar ne akayi mata haka. Wani dan sanda ma a nan ake tsinci gawar sa.

” Iyaye da dama su sha su kai farmaki wadannan wurare domin ceto ‘ya’yan su a wajen shaye-shaye da ‘ya’yan su mata da suka fada harkar karuwanci.

Bincike da gwamnatin Barno tayi kan wadannan matsaloli, ya nuna cewa muddun ba a dau mataki na gaggawa ba toh za a fada cikin matsanancin hali da matsala a jihar.

Abin da ya faru da wadannan wurare shine tun asali ma’aikatar sufurin jiragen kasa ne suka siyar wa ‘yan kasuwa, su kuma suka giggina irin wadannan wurare da ya zama alakakai.

Sannan kuma su kansu masu wadannan gidajen tambadewa sun amsa laifukan su sannan suna rokon a dan kara musu lokaci domin su tattara komatsen su su kara gaba.

Share.

game da Author