Makomar matan Najeriya da ake jigila da sunan aikatau zuwa Saudiyya

0

An dade ana yaudara, damfara, ribbata da zambar matar Najeriya, musamman na Arewacin Najeriya, da sunan kai su kasar Saudiyya su nemi kudi ta hanyar yin aikatau a gidajen Labarawa.

Sai dai kuma wannan hanya ta yi kamari da muni sosai, bayan hawan gwamnatin APC cikin 2015.

Da ya ke a Arewacin kasar ana dokin da zumidin gwamnagtin Buhari a farkon hawan sa, sai aka rika jingina wannan harka ko harkalla da gwamnatin Muhammadu Buhari.

Mata ko maza da dama sun rika bin mata su na yi musu romon-baka da romon kunne cewa, duk mai bidar tara dukiya lokaci guda, to rabon sa na can Saudiyya, ya garzaya kawai ya kwaso.

Haka aka rika yin amfani da sunan gwamnatin Buhari, ana cewa ita ce ta ce a kwashi jama’a ‘bi-la-adadin’ a samar musu aiki a Saudiyya, sai da ta kai a cikin 2016 daya daga cikin hadiman gwamnatin Shugaban Kasa ya fito ya karyata wannan magana.

Sai dai kuma aikin gama ya rigaya ya gama, domin an wayi gari wasu kamfanonin bogi sun bayyana a Kano da Kaduna da Abuja, sun rika buga tandar sayen fam da zuwa intabiyu da nufin duk “wanda Allah ya tsaga da rabon sa, to ya garzayo a cika fam.”

Aka rika yi wa wasu fafalolon makudan kudaden da suka biya, wasu mata kuma masu yawa da suka hada da tsoffi, madaidaita da saffa-saffa, aka rika safarar su, jigila da karakainar kai su Saudiyya ana jibgewa a can.

Sai bayan an kai su can su ke gane cewa ashe dai kuikuyo da barewa ba jinsi da yaba ne.

Sun rika cin azaba, musgunawa, bautarwa da kuma ci musu zarafin da ba su iya tunkarar gwamnati su kai kukan su.

Ladidi (mun boye sunan ta na gaskiya), wata mata ce mai sauran jini a jika, da ke aure a Kaduna, har ta na da danta daya. Ko da ya ke a baya ta haifi wasu biyu, amma duk sun mutu.

An yi mata hudubar-shaidan, ta titsiye mijin ta, sai ya ba ta takardar sakin auren ta, ta na so ta jaraba sa’ar neman arziki, a Saudiyya.

Haka ba da son ran sa ba, mijin ya ba Ladidi takarda, ita kuma ta tarkata kayan dakin ta, ta kira dan gwangwan ya yi musu kudin-goro, ya biya, ita kuma ta sheka ‘Kasa Mai Tsarki’ neman arziki.

A yau ba gobe ba, Ladidi na cikin matan da ke da-na-sani ba su tafi Saudiyya neman kudi ba.

Sau da dama matan da ke can ana gallaza musu, sukan turo bidiyo ko muyar su su na bada labarin irin wahala da azabar da suke sha a hannun Larabawa da takadaran ‘yan Bangaladesh, India da sauran su.

Rahotanni na nuna cewa akwai masu ilimin da bai wuce difloma ko aikin nas-nas da kan samu aiki a wasu garuruwa ko kauyukan Saudiyya.

Amma hakikanin gaskiya yawancin game-garin mata jamhurun masu neman tara kudi ido rufe, duk sukan fada hannun ‘yan harkalla, masu tura su gidajen da za su rika yin aikatau da bai wuce rainon kananan yara ko wanke-wanke da goge ba.

Irin wadannan matan sun sha turo sakonnin yadda ake gallaza musu da duka, musgunawa, tozartawa da sauran cin zarafin da ya hada da fyade.

Akasarin su babu wata dabarar da za su iya yi su dawo Najeriya, domin ana kwace fasfo din su ne idan sun isa kasar.

Abin ya yi muni, har ta kai an rika zargin ofishin Jakadan Najeriya a Saudi Arebiya cewa da sanin su ake wannan harkalla. Wasu ma sun yi ittifakin cewa da su ake yin kashe-mu-raba.

Sai dai kuma Jakadan da kan sa ya karyata wannan zargi, ta hanyar kare kan sa da kuma kare ofishin sa.

Jakadan Najeriya a Saudiya ya kare kan sa da ofishin sa

Jakadan Najeriya a Saudiyya, Isa Dodo, ya karyata zargin da wasu ke yi cewa da hadin bakin sa ake safarar mata daga Najeriya ana kai su Saudiyya su na yin aikatau.

Dodo ya karyata wannan zargi ne a wata hira da aka yi da shi a Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a ranar Labara.

Ya ce babu ruwan Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya da kuma kuma hi kansa da ofishin sa a harkallar kai mata masu aikatau zuwa Saudiyya.

“Na samu labarin wasu ejan na Najeriya su na safarar mata su kai su Saudiyya suna aikatau a gidaje sun a yin aikatau.

Ya ce masu yin wannan harkallar su na yi ne ba tare da sanin Ma’aikatar Harkokin Waje a Abuja ba, ko kuma ofishin sa da ke Riyad, Saudi Arabia.

Yayin da ya ke jan hankalin jama’a, ya kara da cewa an ce tun sama da sheara uku ake wannan safarar mata, to amma shi watan sa bakwai kadai da akama aiki.

Share.

game da Author