Mutane 10 sun rasu a hadarin mota a titin Kano-Kaduna

0

Akalla mutane 10 suka rasu a hadarin mota da ya auku a titi Kano zuwa Kaduna bayan motoci uku sun yi karo da juna.

Kamar yadda shugaban wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haddura FRSC Idris Yahaya ya bayyana wa manema labarai ya ce mutane 9 sun kone a wurin nan take, inda mace daya ta rasu a asibiti.

Hadarin ya auku ne a daidai gaban Kwaleji Kimiyya da Fasaha na Nuhu Bamalli dake Zaria.

” Da direbobin da suka sami rauni da sauran fasinjojin da suka ji ciwo duk an kai su asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake shika Zaria.

” Bayan haka kuma ina kira ga mutane da direbobi da su yika hutawa idan suna doguwar tafiya a hanyayoyin mu. Idan ba hutawa suke yi ba za a dunga samun matsala da irin hadarukka kamar haka.”

Share.

game da Author