Dogara na so a bar wa matasa zalla mukaman Karamin Minista

0

Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya bada shawarar a kebe wa matasa zalla mukaman Karamin Minista a kasar nan.

Dogara ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke jawabi a taron bikin murnar amincewa da dokar bai wa matasa damar tsayawa kowane matsayi a zaben kasar nan.

Ya ke dama tun farko a tarihin gwagwarmayar dimokradiyya, fafutika ce ake yi tsakanin wadanda ake damawa da su da wadanda ba a damawa da su.

” Ni ina ganin ba za a ce mun zura jiki sosai ba, idan bayan zaben 2019, muka nemi a rika bai wa matasa mukamin Karamin Minista, kuma ya kasance su kadai za a rika nadawa a mukamin.

” To ina ganin ta haka ne za a kara samun shigar matasa sosai a cikin mulkin kasar nan ana damawa da su.

Dogara ya ce akasarin wadanda aka maida saniyar-wace a siyasa ko a mulkin kasar nan duk matasa ne.

Share.

game da Author