HARIN FILATO: Ba mu ce ramuwar gayya aka yi ba, kazafi a aka yi mana – Miyetti Allah

0

Shugaban Miyetti Allah na yankin Arewa Maso Tsakiya Danlaci Ciroma ya yayi suka da kakkausar murya game da yadda wasu gidajen jaridu a kasar nan suka yi ta yayada cewa wai harin da aka kai wa mazauna kauyukan jihar Filato ramuwar gayya ce na kisan da akayi wa makiyaya.

Ciroma ya ce wannan magana bai taba yin ta ba sannan bai san da ita ba kamar yadda aka yi da yadawa a kafafen yada labarai. Ya ce bai yi hira da wani gidan jarida ba saboda haka bai san inda suka samo wannan magana.

A bincike da muka gudanar game da haka ashe wani dan jarida ne ya kissa wannan magana cewa wai shi Ciroma ya fadi haka inda ya aika wa ‘yan uwansa manema labarai ta shafin guruf din su a WhatsApp.

Daga nan kuma sai suka yada ta ganin cewa shi wannan dan uwa nasu dan jarida ne ya tabbatar musu da samun wannan magana na Ciroma baki-da-baki.

Amma sai dai bayan binciken da aka gudanar, sai aka gane cewa tabbas, akwai gashi a cikin maganar, aka gano cewa Ciroma bai taba yin irin wannan magana ba.

A haka dai har da mu Jaridar PREMIUM TIME sashen mu na turanci da muka dauki labarin kuma muka gudanar da binciken muke janye wannan magana sannan muke rokon yafiya ga kungiyar Miyetti saboda mamayar mu da akayi a kai har muka fada irin haka bayan ashe shi kan shi wakilin mu ya shammace mu ne cewa da shi aka yi magana baki-da-baki bayan ba haka bane shima dauka yayi a jaridar Nation.

Share.

game da Author