Cin Amanar Juna da Jahiltar Addini ne ya kawo Kisan Kabilanci a Najeriya, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Idan fa matsala ta bujuro, babu shakka sai an ajje bambance-bambance a gefe don a shawo kanta.

Hakan shine mafita, idan kuma ba haka ba, Najeriya zata dade a cikin wannan yanayin.

Babu rikicin da yake cin kudi,abunda ya shafi bincike na masu ilimi, kamar fadan makiyaya da manoma a Najeriya. An yi bincike bila-adadin don ganin an gano abunda yake haddasa rikicin, matsayinsa da kuma hanyoyin samar da masalaha a tsakanin masu fadan.

Binciken da masana suka yi, ban sani ba ko shi binciken ne bai samar da mafita ba ko kuma hanyoyin da za a bi masu kyau bane ko kuma gwamnati ce bata yi amfani dasu ba ta yadda ya dace. Wallahu Ta’alah A’alam! Koma dai menene, dole wadannnan kashe-kashe suna bukatar a tsaya tsayin-daka a mayarwa mai hakki hakkin sa.

Duk wanda aka samu da hannu a ciki, lallai ayi masa hukuncin gaggawa ko da nine karewa.

Babu wani addini da ya goyi bayan ‘dansa ko ‘yarsa da yin kisa a duk duniya. Kuma duk kabilar da zata cewa mutanenta su kashe wasu kabilun, babu shakka bata da wani alheri ga jama’a.

Kuma akwai jahilcin addini a tare da ita ko da kabilata ce ta hausawa. Kwanannan na shiga Jos,har nake yabon ‘yan garin da cewa sun gane wasu ne basa son ganinsu cikin zaman lafiya saboda su ci ribar haka don haka garin yayi lafiya.

Ashe nima Allah ne bai kaddara mutuwata ba da wannan matsalar bata ritsa dani ba. Wadanda suka mutu daga cikin mumunai muna musu addu’ar Allah ya hadamu dasu a aljanna. Muna yiwa ragowar musulmin da suke cikin jihar ta’aziyar rasa ‘yan uwa da abokan arziki. Sannan kuma suyi hakuri.

Inaso duk musulmi da kiristocin Najeriya su sani bama sai na Jos ba.Ita fa kasar Najeriya tamu ce ta mu biyu, baka isa ka koreni ba, nima ban isa na koreka ba tunda Allah ne ya kaddaramu a alqarya daya saboda haka babu yadda zamuyi da juna.

Irin wannan rikicin dole sai mun ajje ‘identity difference’ a gefe munsan abun yi amma idan kowa yace zai kare nasa babu ranar da zamu samu kariya a duk inda suke a Najeriya.

To amma na fahimci wasu basu shiryawa zaman lafiyan ba,kodai suna da hannun jari a rikicin ko kuma cin amana,gidadanci da jahilcin addini ne yake damunsu. Babu musulmi bahaushe ko kirista birom da ya isa yace a littafinsa akwai aya daya ma da tace yaje ya kashe mutumin da bai yi masa komai ba. Wannan raina dokokin zamantakewa ne kai tsaye.

Mu dai musulmi bamu da lokacin daukar fansa, muna kira da gwamnati data dauki mataki saboda an zaluncemu.

Mu haka akayi mana tarbiya, addininmu dan zaman lafiya ne saidai idan an shiga matsayin da muka samu hujjar kare kanmu ko ‘yan uwanmu daga nafsi shine zakaji ance ana rikici da musulmai.Shima kuma wannan yana da matakai sosai.

Ina kira da adalan pastoci da limaman musulmi da kuma sarakunan gargajiya na kowanne bangare da su hada kai don shawa kan wannan kisan gilla da akeyi a tsakanin dalibai da talakawansu.

Hakan shine mafita,anyi wannan tsakanin Postor James Wuye da Imam Muhammadu Ashafa a jihar Kaduna kuma an ga tasirin yin haka wajen samar da zaman lafiya. Kuma wani abun sha’awa kowa a cikinsu rikicin ya tabashi.

Imam Ashafa ya rasa ‘yan uwansa guda biyu da malaminsa,pastor wuye kuma ya rasa hannunsa guda daya. Ayi kokari a bude wuraren da za dinga gamuwa domin tattaunawa a tsakanin addinan mu guda biyu a Najeriya sannan kuma a shigo da matasa ciki don sune ‘yan zafin kai. Yin hakan zai yi tasiri sosai idan Allah yaso.

Allah ya kiyaye.

Share.

game da Author