Kungiyoyin matasa a Jihar Adamawa sun yi kira ga Nuhu Ribadu ya fito takarar gwamnan jihar

0

Kungiyoyin matasa a jihar Adamawa sun yi kira ga tsohon shugaban hukumar EFCC Mal Nuhu Ribadu ya dawo ya yi takarar gwaman jihar a zabe mai zuwa.

A sako na musamman da suka tura wa Mal Nuhu, matasan sun bayyana cewa jihar Adamawa na bukatar mutane irin su Ribadu domin samun ci gaban jihar da dawo wa jihar darajar da aka santa da shi.

“ Gogewar sa da fice da yayi wajen ganin an seta al’umma na daga cikin abubuwan da ya sa muke rokon sa ya fito takarar gwamna a jihar domin mu sami ci gaba a jihar kamar yadda wasu jihohi dake da gwamnoni masu irin halin sa ke da.”

Idan ba a manta Nuhu Ribadu yayi takarar gwamna a jihar Adamawa a 2015, sai dai hakar sa bai kai ga ruwa ba domin dan takarar jam’iyyar APC ne ya bi goguwar Buhari ya dare kujerar.

Yanzu matasa da mutanen jihar suna ta yin gungu suna rokon Mal Nuhu ya fito ya dawo gida ya sake neman gwamnan.

Share.

game da Author