Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su maida hankali wajen ganin an tsayar da kashe-kashen rayuka da ake yi a kasar nan hakanan.
Obasanjo ya bayyana hakane a ziyarar jaje da ya kai garin Jos, babban birnin jihar Filato.
Da yake zantawa da gwamnan jihar Simon Lalong, Obasanjo yace babu abin da zai sa a bari ana ta kashe rayukan mutane babu gaira babu dalili sannan kuma gwamnati bata yin komai a kai.
Ya ce dole ne sai an hada karfi da karfe domin ganin an shawo kan wannan bala’i da ya addabi kasa Najeriya.
” Na dade ina fadin cewa dole ne fa sai mun bi diddigi sannan mun gano ainihin musabbabin faruwar wannan kashe-kashe ta ko wani hanya sannan a duba su daki-daki a samar wa mutane da mafita na dindindin.
” Duk wadannan matsaloli mutane ne ke yin su, saboda haka wadannan mutanen ne zasu samar da hanyoyin da ya kamata abi domin kawo karshen rikice-rikicen.