Shugaban asibitin koyar wa na jami’ar Abakaliki jihar Imo Emeka Ogah ya sanar da rasuwar daya daga cikin likitocin asibitin mai suna Canice Ebirim.
Ogah ya sanar da haka ne ranar Laraba wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abakaliki inda ya bayyana cewa Ebirim ya rasu ne a lokacin da ake buga kallon kafa na World Cup tsakanin Najeriya da Ajantina ranar Talata.
” Na sami labarin rasuwar abokin aikin na da karfe tara na dare, ina ji kuwa jiki na yayi sanyi domin kuwa mutuminane matuka sannan ko da muka rabu kafin wasan yana cikin koshin lafiya.
Ogah yace abokan Ebirim da suke tare da shi sun bayyana cewa yayin da suke kwallon ne suka kula cewa Ebrimi bai jin dadin jikinsa wanda hakan ya sa suka gaggauta kai shi asbibiti cikin wannan dare.
” Sai dai kafin likita su gane abin da ke damunsa ne Ebirim ya ce ga garin kunan.”
A karshe Ogah ya ce bashi da tabbacin abin da ya kashe Ebirim amma za su yi shawara da iyalen mamacin domin gudanar da gwajin da zai tabbatar da abin da ya kashe shi.