A yau Laraba ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas Imohimi Edgal ya bayyana yadda suka kama wasu mutane biyu dake badda kama irinta ‘yan sanda suna damfarar mutane a jihar.
Edgal ya bayyana cewa rundunar ta kama Jumoke Mutairu mai shekaru 45 da Uzoma Johnson mai shekaru 29 sanye da tufafi irinta jami’an ‘yan sandan jihar ranar 20 ga watan Yuni a unguwan Alakara.
Ya ce Jumoke da Uzoma sun bayyana wa jami’an tsaron cewa sun kai shekaru 15 suna gudanar da irin wannan ta’asa a jihar tare da wani shugaban su wanda kuma ke shugabancin cocin ‘Chosen Ministry Church’ a jihar mai suna Johnson O Oni.
Edgal ya ce Jumoke ta bayyana cewa Johnson ya dauke su ne da sunan masu tsaron cocin sa da farko sannan sukan taimaka wurin siyar masa da wasu kaya.
” Dana fara aikin ban taba daukar kai na a matsayin ‘yar sanda ba sai dai a matsayin ma’aikaciyar tsaro wace ke wayar da kan mutane game da illoin aikata miyagun aiyukka.
” Sannan ba mu da albashi illa dan kyauta da muke samu daga cinikin wadannan kaya da muke saidawa.”
Edgal ya kara da cewa rundunar na kokarin ganin ta kamo shugaban su, wato Johnson sannan ya jinjina wa jami’an da suka kamo wadannan mutane.
Discussion about this post