Shugaban hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa (NDLEA) na jihar Kano Hamza Umar ya bayyana cewa a watanin shida da suka wuce hukumar ta kama masu siyarwa da shigo da miyagun kwayoyi 290 a jihar.
Ya sanar da haka ne wa manema labarai ranar Talata a Kano.
Umar ya bayyana cewa a cikin watanni shida hukumar ta gurfanar da wadanda ta kama da miyagun kwayoyin a babbar kotun jihar, sannan hukumar ta kai mutane 117 asibiti a dalilin illar da shan kwayoyin suka yi musu.
” A takaice dai hukumar ta sami nasarar kama kwayoyin da suka kai giram 7,061.582 a cikin watanni shida da suka wuce.
A karshe ya yi kira ga sauran hukumomi masu farautar masu safarar miyagun kwayoyi da su taimaka musu domin ganin an kawo karshen haka a jihar.
Discussion about this post