FADUWAR DALIBAN NAJERIYA JARABAWA: Za a binciki makarantun kasashen waje

0

Gwamnatin tarayya ta umurci kungiyar likitocin hakora (MDCN) da ta binciki dalilin da ya sa daliban da suka yi karatu a makarantun dake kasashen waje suka fadi jarabawar kwarewa na likitoci da akayi a kwanakin baya a kasar nan.

A shekarar 2017 ne daiban da suka yi karatun aikin likita jami’o’in dake kasashen waje su 501 suka rubuta jarabawar kwarewa na akin likita a asibitin koyarwa na jami’ar Ilori, jihar Kwara.

Bayanai sun nuna cewa dalibai 132 cikin 501 ne su suka sami nasarar cin jarabawar.

A kwanankin baya idan za a tuna, iyayen daliban da suka fadi jarabawar sun zargi MDCN da kada ‘ya’yan su da gangar in da har sai da gwamnatin ta umurci kungiyar ta binciki musabbabin faduwar daliban.

” Akwai yiwuwar wadannan dalibai sun yi karatu ne a irin makarantun da kan yaudari iyaye da ‘ya’yan su ne, inda bayan sun tafi can ba za su sami yin karatun kirki ba sannan kuma kaga sun kammala karatun cikin dan kankananin lokaci.

” A inda za ka gane haka shine ko bayan wannan korafi da iyaye suka yi ta yi mun sake shirya musu jarabawar kuma ile duk sun saki fadi.” Cewar Karamin Ministan kiwon lafiya Osagie Enahire.

A karshe rajistaran MDCN Tajudeen Sanusi ya ce kungiyar za ta yi kokarin ganin ta shawo kan wannan matsalar sannan za a ba daliban dama su koma makaranta domin samun kwarewar da ya kamata.

Share.

game da Author