INEC ta yi alkawarin ingantaccen zabe a Ekiti da Osun

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayar da tabbaci ga a ranar Litinin ga ‘Yan Najeriya cewa, za ta gudanar da ingantaccen zabe a zaben gwamnoni da za’a yi a jihohin Ekiti da Osun.

Ta kuma yi alkawarin gudanar da hakan a babban zabe na kasa da za’a yi a kakar zabe ta shekarar 2019.

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ya bayar da wannan tabbaci a yayin da yake jawabin bude taro na horas da ma’aikatan hukumar zabe sanin makamar aiki, tare da hadin gwiwar Cibiyar Tabbatar da Samar da Sahihin Zabe ta Tarayyar Turai, wanda ya gudana a birnin Legas.

Mahmood Yakubu ya kara da cewar, hukumar ta shirya sosai wajen tunkarar babban zabe da za’a yi ta shekarar 2019 inda wannan zabe zai kasance zabe mai cike da tsafta a tarihin zabukan kasar nan.

Shugaban hukumar ya kara da cewar dukkanin tsare-tsare da shirye shirye sun yi nisa a hukumar wajen ganin zaben shekarar 2019 ya fi inganci da tsari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2015.

“Ya na daga cikin abin da ya tara mu a wannan waje shi ne tabbatar da dukkanin matakan da za mu dauka a yayin gudanar da zabukan da ke fuskanto mu”.

“Kuma dukkanin wadannan matakai na zuwa ne bayan kammala dukkanin tsare-tsare na shirin zabukan da ke tafe”. Inji shi.

Share.

game da Author