An canja Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Filato Undie Adie

0

A yau ne Talata, aka bayyana cewa an cire Undie Adie daga matsayin Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Filato, an maye gurbinsa da Bala Ciroma.

Ciroma ya karbi aikin ne daga Undie Adie, wanda shi kuma aka ba shi umarnin cewa ya koma hedikwatar ‘yan sanda ta Abuja da gaggawa.

Kakakin ‘yan sandan Filato, Terna Tyopev, ya tabbatar da isar sabon kwamishinan ‘yan sandan, wanda ya ce tuni har ya karbi aiki daga hannun Andie tun da sanyin safiya.

Kafin a maida Ciroma a matsayin kwamishinan ‘yan sandan Filato, shi ne Mataimakin Kwamishina mai kula da binciken rikakkun masu laifuka da kuma sha’anin leken asiri a hedikwatar Abuja.

Ya kuma taba yin aiki a matsayin shugaban bincike a Hukumar EFCC, a Abuja.

Share.

game da Author