RIKICIN FILATO: Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Filato yau

0

A yau ne Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Filato domin gane wa idon sa irin barnar da kashe-kashen da aka yi a jihar ya yi muni.

Zai je ne kuma domin yin ta’aziyya da jaje ga wadanda rikicin ya shafa.
A yanzu dai shugaban ya na jihar Cross River inda zai kaddamar da wani aiki.

A jiya Litinin ne Buhari ya tura Mataimakin sa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar gaggawa jihar Filato.

Mutane da dama sun soki lamirin yadda shugaban ya ki garzaya da kan sa, sai ya tura wakilci a jiya Litinin.

Majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tuni wata tawagar Buhari ta tashi daga Abuja inda ta yi gaba zuwa jihar Filato, inda Buhari zai iske su a can idan ya tashi daga Calabar nan ba da jimawa ba.

Share.

game da Author