Kwanaki biyu kafin kisan da aka yi wa mazauna Barkin Ladi a lokacin da suke wani zaman makoki, an kashe wasu Fulani ‘yan kasuwa su hudu a yankin.
Dama kuma PREMIUM TIMES ta buga rahoton yadda aka tare Fulanin a kan titi, su hudu aka kashe su, sannan aka kone motar su, a kan hanyar su ta dawowa daga wata kasuwar kauye.
YADDA AKA FARA KASHE FULANIN A HIAPANG
Kisan ya faru ne da yammacin Alhamis da ta gabata, a lokacin da Fulanin ke kan hanyar su ta dawowa daga cin wata kasuwar sayar da shanu. An yi musu kwanton-bauna, aka kashe su.
Washegari sai Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Karamar Hukumar Barkin Ladi, ya zargi matasan yankin na Barkin Ladi da laifin kashe Fulanin a Hiapang kusa da shiga garin Barkin Ladi.
Abubakar Gambo ya kuma zargi wadanda suka yi kisan da dauke gawarwakin wadanda suka kashe, suka gudu da su.
“Kisan da suka yi wa ‘yan uwan mu ya faru ne tsakanin 6:30 zuwa 6:40 na yamma a ranar Alhamis. ‘Yan kabilar Birom ne suka tare su, suka kashe su, sannan suka kone motar da suke ciki. A lokacin sun ci kasuwar Bukuru ne sun dawo. Sun kuma gudu da gawarwakin su.
Shi dai sakataren kunyar ta Miyetti Allah ya ce sun kai rahoton kisan ga ‘yan sanda.
“Wadanda ‘yan kabilar Birom din suka kashe, dukkan su su na da iyali. Akwai Bala Adamu, Isa Mohammed, Ibrahim Ahmed da Lawal Abubakar Dangana.
“Jami’an tsaro na JTF sun garzaya wuri, amma a lokacin da suka isa, sun samu motar ta na cin wuta.
“Wannan ne karo na uku da matasan Birom na kai mana hari su na kashe ‘yan uwanmu.”
Lokacin da PREMIUM TIMES ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Filato a ranar Juma’a, kafin Fulani su kai harin ramuwar-gayya, ‘yan sanda sun ce ba za su iya cewa an kashe Fulanin ba, sai dai su ce an gudu da su an yi garkuwa, domin an gudu da su din.
Sai dai wani shugaban wata kungiyar matasan kabilar Birom mai suna Dalyop Choji, ya ce babu ruwan ‘yan kabilar Birom da yin kisan, domin daga wani wuri aka biyo wadanda aka kashe din da mota kirar Vectra, aka bude musu wuta, san aka tilasta motar su ta tsaya.
Wannan kisa shi ne ya haddasa Fulani yin samame suka kai mummunar ramuwar-gayya, inda kuma washegari kabilun yankin Jos suka rika tare hanya sun a kashe masu wucewa da suke ganin musaulmai ne.