POLIO: Har yanzu kasashen Afrika na fama da cutar kamar ba a magani

0

Kungiyar yaki da cutar shan inna (POLIO) na kasashen Afrika (ARCC) ta koka kan yadda har yanzu cutar taki ci taki cinyewa a kasashen Afrika.

Kungiyar ta bayyana haka ne a taron kawo karshen ci gaba da yaduwar cutar da aka yi a babban birnin tarayya, Abuja cewa rahoyon binciken da tayi ne ya nuna mata haka a wsu kasashen Afrika.

Kungiyar ta ce kasashen Afrikan da suke fama da wannan matsalar sun hada da Kenya, Equatorial Guinea, Guinea Bissau, Angola, South Sudan, Central Africa republic, Madagascar, Lake Chad Basin, Congo, Nigeria da wasu da dama.

A karshe ARCC ta yi kira ga wadannan kasashe da su mai da hankali wajen ganin sun yi wa yara kanana da ke bukatar rigakafin allurar tun da wuri domin ganin an kawo karshen cutar kwata-kwata a kasashen.

Share.

game da Author