RASHA 2018: Maradona ya garzaya shirya wa su Messi tuggun yadda za su ci Najeriya

0

Tsohon dan wasan Ajantina, kuma tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafar kasa, Diego Maradona, ya nemi iznin yin ganawar sirri da ‘yan wasan kasar kafin karawar su da kungiyar Super Eagles da za su yi gobe Talata.

Ajantina dai ba za ta iya wucewa zuwa zagayen wasa na gaba ba, har sai ta doke Najeriya da cin kwallye da yawa.

Sai dai kuma ita Najeriya za ta ita wucewa zuwa wasa na gaba, ko da kuwa kunnen doki ta yi da Ajantina.

Maradona dai ya ce idan aka ba shi iznin ganawa da ‘yan wasan, to zai je wurin su ne tare da rakiyar wasu tsoffin fitattun ‘yan wasan kasar wadanda suka taka wa Ajantina rawar gani a idon duniya a lokacin ganiyar su.

“Kun ga dai zan tafi da tsohon mai tsohon mai tsaron gida, Nery Pumpido, Sergio Goycochea, Claudio Caniggia, Daniel Passarella, kai har da Jorge Valdano.” Haka Maradona ya shaida wa gidan talbijin na Venezuela, mai suna Telesur.

“Za mu je necdomin mu kare martabar kasar mu. Mun shiga gargarar kakarin mutuwa saboda wulakancin da muka kwasa a hannun kasar Croatia. Muka tashi har yau ko kwallon bogi ba mu jefa a kowace raga ba.

“Duk wani mai kishin saka rigar kasar Ajantina, ya fusata sosai yadda Croatia ta wulakanta mu. Kasar da ba Spain ko Jamus ko Brazil Holland ba, haka kawai ta kwance mana zani a kasuwa.” Inji Maradona.

Idan za a iya lura, Segun Adegbami da Kanu Nwanko sun je sun yi wa ‘yan wasan Najeriya huduba, a lokacin da za su kara da Iceland, bayan da Croatia ta yi nasara a kan Najeriya da ci 2-0.

A daya gefen kuwa, ‘yan wasan Najeriya sun kara shan alwashin cewa ba za sub a Najeriya kunya a wasan sun a ko a ci ko a dawo gida da za su kara da Ajantina a gobe Talata ba.

Share.

game da Author