TINUBU GA OBASANJO: Ka na yi mana shiga sharo ba shanu a APC fa, babu ruwan ka da harkar mu

0

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya gargadi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya maida hankalin sa ga abinda ke gaban sa kawai, ya daina saka bakin sa a abinda bai shafe sa ba musamman harkokin jam’iyyar APC.

” Haba kadifirin Obasanjo yayi yawa. Amma sannin kowa ne cewa nasarorin da aka samu a mulkin Buhari cikin shekaru 3 da suka wuce ya zarce wanda aka samu a shekaru 16 na mulkin PDP a kasar nan.
Kawai ya zo sai yi mana katsalandan ya yake yi a harkoki.

” Mu ba bukatar sa muke ba, ya tafi can ya ci gaba da harkokin sa.

” Godiyan mu daya Allah ya sa shi (Obasanjo) ba dan jam’iyyar APC bane. A sani na ma ya dade da kekketa katin jam’iyyar sa ta PDP tun tuni. Ya daina yi mana kadifiri a harkokin mu kawai.

Bayan haka ya jinjina wa shugaba Buhari da ya bayyana ra’ayin sa na yin takara a karo na biyu, cewa hakan yayi daidai, kuma babu shakka shine zai lashe zabe a 2019.

Tinubu ya yabawa kokarin da mataimakin shugaban kasa yake yi a kasar nan sannan kuma ya yi wa sabon shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole addu’ar fatan alheri a tsawon mulkin sa.

Share.

game da Author