Dalilin da ya sa na kaurace wa gangamin APC – Kwankwaso

0

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba haka kawai bane ya kauracewa taron gangamin zaben APC da aka yi a Abuja tun ranar Asabar.

Kwankwaso ya ce gudun a samu tashin hankali ne ya sa shi da jama’ar sa suka ki halartar taron.

” Na farko dai uwar jam’iyyar da ta wuce bata amince da zababbun wakilai na bangaren mu ba. A dalilin haka muka ga tunda ba a amince da na mu wakilan ba, idan muka zo za a iya samun baraka a wajen taron

” Kowa ya ga abinda ya faru a rumfunar Jihohin Imo da Delta inda aka yi ta kai ruwa na tsakanin wakilan bangarori biyu. Akayi kacakaca da kujerun rumfunar sannanwasu ma suka sami rauni.

” Da mun zo da kila abin yafi nasu muni, shine yasa kawai muka ce a hakura a kaurace wa taron.

Kwankwaso ya kara da cewa yana yi wa sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar fatan alkhairi da fatan Allah yasa su iya hada kan jam’iyyar.

Idan ba a manta ba da yawa cikin ‘yan kungiyar sabuwar PDP basu halarci wurin gangamin ba sai dai kuma an kammala taro lafiya sannan tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ne aka zaba sabon shugaban jam’iyyar APC din.

Share.

game da Author