RASHA 2018: Ingila ta yi wasan kura da Panama

0

Harry Kane ya zama dan wasa na uku da ya ci kwallo uku a wasa daya, a Gasar Cin Kofin Duniya wadda ke gudana a kasar Rasha.

Kane ya ci kwallaye uku sa wasan da Ingila ta buga yau Lahadi da Panama.

Kwallayen uku dai biyu da bugun daga kai sai mai tsaron gida, wato fanereti ya samu nasanar jefa su.

Dama kuma a wasan Ingila na farko sun yi nasara a kan kasar Tunisiya, wanda wannan nasara ta biyu da Ingila ta yi, ya ba ta damar hayewa zuwa zagaye na biyu.

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo ne ya fara cin kwallaye uku, sai kuma Romeleu Lukaku na kasar Belgium da ya ci uku jiya.

A ci 6-1 da Ingila ta yi wa Panama, dan wasa John Stone ma ya jefa kwallaye biyu a ragar Panama.

Share.

game da Author