KASHE-KASHEN ZAMFARA: Marafa, Yari, Dambazau sun bude babin dora wa junan su laifi

0

A jiya Juma’a ne jami’an gwamnatin tarayya da na jihar Zamfara suka bude babin dora wa juna alhakin kisan gillar da mahara ke yi wa mazuna yankunan karkarar jihar Zamfara.

Sanata Kabiru Marafa daga jihar Zamfara, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da ikirari da kuma matsayar sa cewa Gwamna Abdul’Aziz Yari ne ke da laifin kasa magance maharan jihar.

A cikin shekara kadai an kashe daruruwan mutanen karkara a jihar Zamfara.

Marafa ya ce ya sha yi wa gwamna Yari shawarwarin yadda za a magance kashe-kashen da ake yi a Zamfara.

“Amma maimakon ya yi ammfani da shawarwari na, sai ma ya dauke ni wani rikakken abokin gabar sa.”

Jama’a da dama a fadin kasar nan su na korafin yadda gwamna Yari ba ya iya zama a jihar Zamfara, duk kuwa da irin kalubalen da jihar ke fuskanta, amma kullum ya na Abuja, maimakon ya tsaya ya magance matsalar jihar sa.

Yayin da a Zamfara ne aka fi yin kashe-kashe, a wani gefen kuma ana ganin cewa Yari ya fi kowane gwamnan kasar nan rashin zama ya yi aiki a jihar sa.

Cikin makon nan ne Ministan Harkokin cikin gida Janar Dambazau (Mai Ritaya) ya bayyana cewa gwamnoni su rika tsayawa jihohin su su na yi aikin da ya zame musu wajibi, su daina dora wa gwamnatin tarayya kasa magance tsaro a jihar su.

“Matakin farko na kawo karshen kashe-kashen shi ne gwamna Yari ya damka makusantan sa da ke da hannu a kashe-kashen, domin a hukunta su.

“Hanya ta biyu kuma ita ce Yari ya daina gallafiri zuwa Abuja da bilumbituwa zuwa kasashen waje, ya tsaya ya daina yawo, ya zauna Zamfara ya magance matsalar jihar.

Kwanan nan ne Yari ya ce ba ya iya tabuka komai dangane da magance matsalar Zamfara, domin jami’an tsaro ba a hannun sa suke ba.

Share.

game da Author