Ban yi amanna da Obasanjo da Buhari 100 bisa 100 ba – Soyinka

0

Fitaccen dan taratsi Wole Soyinka, ya bayyana dalilin da ya sa bai yi amanna da Obasanjo da Shugaba Muhammadu Buhari 100 bisa 100.

Da ya ke amsa tambayoyi a wurin wani taro, ya bayyana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin munafikin da ke saurin sauya launi tamkar hawainiya.

“Ba a taba yin munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba.”

Ya yi wannan bayani a wurin taron ranar ‘yan jarida ta dunya a babban dakin taro na otal din Hilton a Abuja.

An tambaye shi me ya sa ya tsani Obasanjo, ya ce ba wai tsanar saya yi ba, amma saboda munaficcin sa ne ya sa ba ya ganin kan Obasanjo da gashi.

Da ya juya kan shugaba Buhari, shi ma ya buga masa tambarin munaficci, inda Soyinka ya bayyana cewa, “Ya za a yi Buhari da ke babatun yaki da cin hanci, amma a gefe daya ya rika yabon Abacha, ya na kare shi ya na cewa bai saci kudin Najeriya ba?”

Soyinka ya ce duk mutumin da ke kare gwamnatin Abacha ya na cewa ba a saci kudi ba, to ba zai dauki al’amurran wannan mutum da gaske ba, ko ma wane ne.

Idan ba a manta ba, gwamnatin Buhari ta karbo tsabar kudade har dala milyan 321 daga cikin kudaden da Abacha ya handame ya kimshe kasashen waje kafin ajalin sa.

Duk da wannan, bai hana kusan sau uku Buhari na cewa Abacha ba barawo ba ne.

“ Abacha shi ya daure Abiola da mtane da dama. To don me za ka bai wa Abiola lambar gimamawa saboda zaluncin da ka ce an yi masa, amma kuma ba za ka kira wanda ya yi masa zaluncin a matsayin azzalimi ba?

Ya kara tunatar da kashe su Ken Saro Wiwa da Abacha ya sa aka yi.

Share.

game da Author